A cikin shekarun nan da suka wuce, an bunkasa harkokin dab'i ta hanyar digital cikin sauri a kasar Sin. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, yawan kudi da kasar Sin ta samu daga wajen harkokin ya wuce kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 20 a shekarar bara. Yin amfani da fasahar digital wajen buga jaridu da mujalloli da makamantansu wata sabuwar hanya ce da kasar Sin ke bi wajen bunkasa harkokin buga jaridu da mujalloli da makamantansu.
Yanzu, a kasar Sin akwai mutane da yawa wadanda ke karanta jaridu da littattafai ta hanyar Internet ko ta wayar salula. Malama Chen Yi mai shekaru 24 da haihuwa a bana tana aiki a wani kamfanin IT na Beijing, babban birnin kasar Sin. Ta bayyana cewa, tana sha'awar karanta littattafai ainun, ta kan yi kwofin littattafai da ke kan tashar Internet. Ta ce, tana karanta irin wannan littattafai cikin sauki, idan an kwatanta su da littattafan takardu. Ta kara da cewa, "Ina sha'awar karanta littattafai sosai. Na kan yi kwafin littattafai da ke kan Internet don karanta su, A ganina, a iya karanta littattafai da ke kan Internet ta hanyar wayar salula ko na'ura mai aiki da kwakwalwa yadda aka ga dama, don haka ana karanta littattafai da ke kan Internet cikin sauki, idan an kwatanta su da littattafan takardu. Sa'an nan kuma ana daukarsu cikin sauki."
1 2
|