Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-03 18:57:58    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya tashi ziyarar Australia da kuma halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC

cri

A lokacin ziyararsa, shugaba Hu zai yi ayyuka da dama. Malam He ya yi karin bayani kan muhimman harkoki da ke cikin ajandar shugaba Hu, ya ce,'A lokacin ziyararsa, shugaba Hu zai yi shawarwari da gwamnan kasar da firayim ministan kasar da shugabannin majalisun dattijai da wakilai na kasar da shugaban jam'iyyar 'yan kwadago da sauran shugabannin Australia, inda za su yi musayar ra'ayoyinsu kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Australia da manyan al'umuran duniya da yankuna da ke jawo hankulansu dukka. Zai kuma ziyarci jihohin Australia ta Yamma da New South Wales, zai zanta da mutane na rukunnoni daban daban na kasar. Sa'an nan kuma, a lokacin ziyarar Hu, hukumomi da masana'antun da abin ya shafa na kasashen 2 za su daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da yawa game da tattalin arziki da ciniki da aiwatar da dokoki da makamashi da albarkatu da kimiyya da fasaha.'

Halartar taron koli na kungiyar APEC wani muhimmin aiki ne daban da shugaba Hu zai yi a wannnan karo. Malam Cui Tiankai, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin ya yi karin bayani kan ajandar shugaba Hu wajen halartar taruruka, ya ce,'Shugaba Hu zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabanni da taron tattaunawa a tsakanin shugabannin da wakilan kwamitin ba da shawara kan masana'antu da kasuwanni na kungiyar APEC wato ABAC da taron koli kan harkokin kasuwanci na kungiyar APEC. A gun taron shugabanni, shugaba Hu zai bayyana ra'ayi da matsayin da kasar Sin ke tsayawa a kai kan ci gaban hadin gwiwar Asiya da tekun Pacific da sauye-sauyen yanayi. A gun taron koli kan harkokin kasuwanci na kungiyar APEC, shugaba Hu zai bayyana ra'ayin kasar Sin kan al'amuran da ke jawo hankula a fannin bunkasuwar tattalin arzikin duniya da Asiya da tekun Pacific, zai kuma yi karin bayani kan halin da kasar Sin ke ciki a fannin bunkasuwar tattalin arziki. A lokacin tarurukan, zai yi shawarwari da shugabannin wasu mambobin kungiyar.'

A gun taron koli na kungiyar APEC da za a yi a wannan karo, kasar Australia da ke matsayin mai masaukin taron ta mayar da batun sauye-sauyen yanayi a matsayin daya daga cikin muhimman batutuwa, za a kuma yi tattaunawar musamman a kansa a gun taro na mataki na farko. Game da wannan, malam Cui ya ce,'Kasar Sin tana fatan 'sanarwar Sydney' game da sauye-sauyen yanayi da za a daddale da kuma bayar da ita bisa tushen ra'ayi daya da yawancin mambobin kungiyar za su samu a gun taron shugabanni za ta nuna cewa, mambobin kungiyar APEC suna nuna ra'ayi mai yakini wajen daidaita sauye-sauyen yanayi tare.(Tasallah)


1 2