Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-03 18:57:58    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya tashi ziyarar Australia da kuma halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC

cri

Yau ran 3 ga wata, shugaban Hu Jintao na kasar Sin ya tashi zuwa kasar Australia daga nan Beijing don kai ziyarar aiki da kuma halartar kwarya-kwaryar taro na karo na 15 na shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da tekun Pacific wato taron koli na kungiyar APEC. Wannan shi ne muhimmin matakin diplomasiyya da shugaban kasar Sin ya dauka a gabannin babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, shi ya sa ya jawo hankulan mutane sosai. Babban jami'in ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Hu zai yi za ta sa kaimi kan bunkasuwar huldar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Australia daga dukkan fannoni yadda ya kamata cikin dogon lokaci. Ban da wannan kuma, a gun taron koli na kungiyar APEC, shugaba Hu zai bayyana ra'ayin kasar Sin kan ci gaban hadin gwiwa a tsakanin yankunan Asiya da tekun Pacific da sauye-sauyen yanayi da al'amuran da ke jawo hankula a fannin bunkasuwar tattalin arzikin duniya da Asiya da tekun Pacific.

A kwanan baya, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin malam He Yafei ya yi wa wakilinmu bayani kan makasudin ziyarar da shugaba Hu zai kai wa Australia da kuma ma'anarta. Ya ce,'Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 35 da Sin da Australia suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu. Makasudin ziyarar aiki da shugaba Hu zai kai wa Australia shi ne don kara amincewa da juna da kyautata ra'ayoyi daya da suka samu da zurfafa hadin gwiwarsu da kuma samar da kyakkyawan makoma tare. Mun yi imanin cewa, wannan ziyara tana da muhimmanci sosai wajen kyautata cudanya a tsakanin manyan jami'ansu da sa kaimi kan yin mu'amalar sada zumunci da kyautata hadin gwiwar a-zo-a-gani da kuma raya huldar hadin gwiwarsu daga dukkan fannoni yadda ya kamata cikin dogon lokaci.'

1 2