
Tun daga karni na 14 zuwa na 19, an sami bunkasuwa sosai wajen yin tangaran a birnin Jingdezhen. An kafa masana'antu a wannan gari musamman domin yin tangaran da ake samar da su ga fadar sarkin kasar Sin, ta haka garin Jingdezhen ya fara samun wadatuwa kwarai har ba a taba samun irinta ba a da. Sa'an nan an fitar da tangaran na wannan gari zuwa nahiyar Asiya da ta Afrika da Turai da kuma Amurka, har ila yau kuma wasu kasashen Turai ta yamma sun yi odar tangaran daga masana'antun yin tangaran na fadar sarkin kasar Sin a wancan zamani. Haka zalika an fitar da fasahar yin tangaran mai launin shudi da aka yi musu kyakyawan ado zuwa kasar Korea da Japan da Iran da Vietnam da Syria da Masar da kuma Italiya da dai sauran kasashe.
Yayin da ake bunkasa sana'ar yin tangaran a cikin dogon lokaci a birnin Jingdezhen, an fitar da kyawawan tangaran iri dabam daban wadanda aka yi musu ado mai kyaun gani, wadanda kuma ke da daraja kwarai.(Halilu) 1 2 3
|