Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-29 15:28:01    
Garin Jingdezhen, shahararren gari ne da ke fitar da tangaran

cri

Garin Jingdezhen da ke a kudancin kasar Sin ya shahara sosai wajen fitar da tangaran a gida da waje. Yau sama da shekaru 1,600 ke nan da aka gina garin Jingdezhen na lardin Jiangxi da ke kudancin kasar Sin, tsohon sunansa shi ne "Changnan".

Tun can shekaru 2,000 da suka wuce, mutanen garin Jingdezhen sun riga sun fara yin tangaran ta hanyar dakin tuya da aka gina a kan tudu. Amma kafin karni na 10, tangaran da aka fitar daga wannan gari bai yi suna a kasar Sin ba. Tangaran na wannan gari ya kai matsayi na farko ne a zamanin daular Song wato tsakanin shekarar 960 zuwa ta 1279.

A farkon zamanin daular Song, an fi yin tangaran mai launin fari a arewacin kasar Sin, haka nan kuma tangaran da aka fi yinsu a kudancin kasar Sin tangaran ne mai launin shudi. Amma a garin Jingdezhen, an fitar da wani irin tangaran mai launin fari da shudi wanda ba a taba ganin irinsa ba a da.


1 2 3