Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-28 15:34:26    
Babbar korama da ke tsakanin Beijing da Hangzhou

cri

Sashen Wuxi na babbar koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou yana maras fadi, haka kuma ruwan na da zurfi. A gabobinsa akwai gine-ginen mazaunan wurin na layi layi. Gadar Qingming aka gina ta a kan babbar koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou a tsakiyar zamanin daular Ming, wato a tsakiyar shekarar 1368 zuwa ta 1644. Ita ce gada mafi girma da aka gina da duwatsu a zamanin da a birnin Wuxi, wadda kuma aka fi adana ta yadda ya kamata. A gaban tsohuwar kofa ta kudu ta wannan birni, masu yawon shakatawa suna iya ganin wata babbar hasumiya mai hawa 7 da ke da kusurwa 8, wadda aka gina a karni na 10, sunanta shi ne Miaoguang. Wannan babbar hasumiya da aka gina a gidan ibada na addinin Buddha na Nanchan ta yi suna ne a kuriyar kogin Yangtze.

Sashen Wuxi na babbar koramar tsakanin Beijing da Hangzhou ya yi fadi a tsakanin kofa ta kudu ta birnin Wuxi zuwa kofa ta arewa ta birnin. A kan sami cunkuson kwale-kwalen katako da aka tuka da gorori, da kananan kwale-kwale da jiragen ruwa a wajen kullum. Bayan da suka more idanunsu da dimbin kwale-kwale da jiragen ruwa da ke ta kaiwa da kawowa a sashen Wuxi na babbar koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou, hakika masu yawon shakatawa za su gamsu da yadda wannan korama mai shekaru dubu da ginawa take cikin kyakyawan yanayi.( Tasallah)


1 2