Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-28 15:34:26    
Babbar korama da ke tsakanin Beijing da Hangzhou

cri

An gina babbar korama daga birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, zuwa birnin Hangzhou, babban birnin lardin Zhejiang. Tsawonta ya kai misalin kilomita 1747 gaba daya. An mayar da ita tamkar wata alamar wayewar kai na gargajiya na kasar Sin, wata daban ita ce Babbar ganuwa. An fara haka babbar korama da ke tsakanin Beijing da Hangzhou tun daga karni na 12 zuwa karni na 11 kafin haihuwar Annabi Isa A.S.. An tsawaita ta da kuma fadada ta a karni na 7 zuwa karni na 14 bayan haihuwar Annabi Isa A.S..

An mayar da birnin Wuxi na lardin Jiangsu a matsayin mafarin babbar koramar da ke tsakanin Beijing da Hangzhou. An haka sashen Wuxi na babbar koramar a tsakanin Wumu a arewa da kuma Wangting a kudu, tsawonsa ya kai misalin kilomita 40, sa'an nan kuma, sashen Wuxi na babbar komarar mai tsawon kilomita 14.6 ya ratsa ta birnin Wuxi. Ko da yake shekaru fiye da 2400 sun wuce, amma har zuwa yanzu, ruwa na gangara a cikin wannan babbar komara. A gabobi 2 na babbar koramar kuma, akwai wuraren yawon shakatawa da kuma wuraren tarihi masu dimbin yawa.


1 2