Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-24 17:26:35    
Cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao

cri

Sa'annan Mr. Zhao Qinghua ya bayyana cewa, da yake cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinghuangdao ta kasance filin wasan kwallon kafa na farko na cikin gidan kasar Sin da aka kammala gina shi domin taron wasannin Olympic na Beijing, don haka, akwai wasu abubuwan da za a kyautata su. A lokacin da mataimakin shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa Issa Hayatou ya kawo ziyarar gani da ido a nan birnin a shekarar bara, inda shi ma ya gabatar da wasu shawarwari masu. Mr. Zhao Qinghua ya kuma kara da cewa, " Mun kuma yi kwaskwarimar filin wasannin bisa bukatun kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing da kuma na wasu hukumomin da abin ya shafa na kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa".

Cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao na da manyan gine-gine guda uku, wato filin wasannin motsa jiki, da dakin wasannin motsa jiki da kuma dakin horar da 'yan wasa. Yanzu, batun yin amfani da ginin cibiyar ya fi janyo hankulan mutane da yawansu ya kai 440,000 kawai na birnin Qinhuangdao. Game da wannan dai, Mr. Zhao Qinghua ya furta cewa: " Lallai mun yi la'akari sosai da wannan batu. Mun gina wani babban kanti a cikin wani ginin dake waje da filin wasannin; Ban da wannan kuma mun gina wasu gidaje domin amfanin kasuwanci, wato ke nan za mu bada hayar wadannan gidaje bayan an kawo karshen gasannin. Dadin dadawa, za mu gina wata cibiyar wasan kwallon tennis, da wata cibiyar wasan tseren gudu da takalma masu taya da kuma wasu kananan filayen horaswa na wasan kwallon kwando da na kwallon tafin hannu. Za a mayar da wadannan gine-gine don su zama wani lambun shan iska na wasannin motsa jiki. ( Sani Wang )


1 2