Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-24 17:26:35    
Cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao

cri

Aminai 'yan Afrika, a cikin shirinmu na makon jiya, mun dan gutsura muku wani bayani a game da makarantar wasan kwallon kafa ta Qinhuangdao. Yau dai, za mu kawo muku wani bayani kan cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao. Tuni a watan Yuli na shekarar 2004 ne aka kammala gina wannan cibiya da kuma soma amfani da ita a hukumance, wadda kuma ta kasance filin wasannin motsa jiki na farko da aka soma gina shi da kuma yin amfani da shi bayan kammala gina shi dake cikin rassan filayen wasa na gasannin kwallon kafa na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao tana bakin teku a unguwar Haigang ta birnin Qinhuangdao. Fadinta ya kai murabba'in-mita 74,600, kuma jimlar kudin da aka zuba wajen gina ta ta kai kudin kasar Sin wato Renminbi Yuan miliyan 150. Wannan cibiyar wasannin motsa jiki na iya daukar 'yan kallo kimanin 30,000; In an duba wanann ginin cibiya mai hawa shida daga nesa, to siffar ginin tana kama da wani kwale-kwale dake tafiya kan teku.

Ya kasance da kyakkyawan tsarin tsaro na zamani a wannan cibiya, inda ke da kyamarorin telebijin 185. Ban da wannan kuma, an kafa wani rumbun tattara bayani a cikin wannan cibiya, wanda yake hada da tsarin sayar da tikitoci da na dudduba tikitocin, wato ke nan daga cibiyar sarrafe-sarrafe ne ake iya duba yadda 'yan kallo suke shiga cikin filin wasan ba tare da taba lokaci ba. Hakan zai iya hana wasu mutane shiga cikin filin wasan dauke da tikitocin jabu. Domin jarraba harkokin duk filin wasannin da kuma bada tabbaci ga gudanar da taron wasannin Olympic lami-lafiya, gwamnatin birnin Qinhuangdao ta taba karbar bakuncin shirya gasanni da dama na gida da na waje daya bayan daya bayan da aka kammala gina filin wasannin.

Mr. Zhao Qinghua, mataimakin babban manajan kamfanin bunkasa wasannin motsa jiki na birnin Qinhuangdao ya bayyana cewa: " Bayan da aka kammala gina wannan filin wasanni, mun dauki nauyin gudanar da wasu gaggaruman gasanni daya bayan daya, kamar taron wasannin motsa jiki na lardi, da gasar wasan kwallon kafa tsakanin wasu mutane taurari da kuma gasannin ja-in-na na wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kasar Sin da kungiyar kasar Japan, da tsakanin kungiyar kasar Sin da kungiyar kasar Thailand da kuma na tsakanin kungiyar kasar Sin da kungiyar kasar Syria ,wadanda aka gudanar a shekarar bara. Mun yi haka ne domin horar da 'yan wasa na kungiyar kasarmu. Ban da wadannan kuma, mun yi gwaje-gwaje domin kyautata ayyukan gudanar da harkokin duk birnin da kuma na filin wasannin."

1 2