Malam Li Yongfu, mataimakin shugaban yankin raya tattalin arziki na birnin Panjin ya bayyana cewa, "mun jawo jari da aka zuba a yankin raya tattalin arzikinmu don kafa wasu masana'antun kera kayayyakin aiki na man fetur. A sakamakon hauhawar farashin man fetur, ana ta bunkasa wadannan masana'antu cikin sauri sosai. Ta haka dai ne, ake ta samu ci gaba cikin sauri wajen bunkasa masana'antun kera kayayyakin aikinmu a birnin Panjin."
Bayan haka, Malam Li Yongfu ya yi hasashen cewa, tun daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, matsakaicin saurin bunkasuwar masana'antun kera kayayyakin aiki na man fetur zai karu da sama da kashi 30 cikin dari a ko wace shekara a yankin raya tattalin arziki na birnin Panjin. Ya ci gaba da cewa, "bisa shirin da muka tsara, tun daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, matsakaicin saurin bunkasuwar masana'antun kera kayayyakin aiki na man fetur zai kai kashi 30 zuwa kashi 50 cikin dari a ko wace shekara. Yawan kudi da za a samu daga wajen samar da kayayyakin aiki na man fetur zai kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 10 a shekarar 2010. Kana za mu mayar da yankin don ya zama yanki mafi girma da ake kera kayayyakin aiki na man fetur a kasar Sin. "(Halilu) 1 2
|