Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-24 17:14:19    
Birnin Panjin na kasar Sin yana raya sansanin kera kayayyakin aikin man fetur na kasar

cri

Birnin Panjin yana kudu maso yammacin lardin Liaoning na kasar Sin, kuma a bakin teku. A sakamakon farfado da tsoffin sansanonin masana'antu da ke a arewa maso gabashin kasar Sin da kokarin raya wuraren tattalin arziki a bakin teku na lardin Liaoning, yankin raya tattalin arziki na birnin Panjin yana kokari sosai wajen raya sansanin kera kayayyakin aiki na man fetur na kasar Sin.

Ya kasance da filin man fetur mafi girma na uku na kasar Sin a birnin Panjin. Amma sabo da yawan gurbataccen man fetur da ake hakowa ya yi ta raguwa a cikin shekarun nan da suka wuce, shi ya sa an gamu da wahala wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin birnin. Malam Chen Haibo, sakataren reshen Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a birnin ya bayyana cewa, "raguwar gurbataccen man fetur da gas da ake hakowa tana kara kawo cikas ga bunkasa harkokin tattalin arzikin birnin Panjin, sabo da haka wani aikin gaggawa da muke fuskanta shi ne yaya zamu iya samu ci gaba mai dorewa wajen raya birninmu mai arzikin albarkatun kasa. Bisa manufar da birninmu ya tsara game da samun bunkasuwa a tsakanin shekarar 2006 zuwa ta 2010, wani babban aiki da muke yi shi ne bunkasa masana'antun kera kayayyakin aiki na man fetur da sauransu"

A shekarar 2005, birnin Panjin ya kafa yankin raya tattalin arziki don neman cim ma manufarsa. A cikin yankin nan, an kebe filaye musamman domin kafa masana'antun kera kayayyakin aiki na man fetur na zamani. Ya zuwa yanzu, wasu manyan masana'antun kera kayayyakin aiki na man fetur sun riga sun kafa kananan masana'antunsu a yankin nan. Alal misali, wani babban kamfanin kera kayayyakin aiki na man fetur da masana'antun kera na'urorin man fetur mai suna Baoji da kamfanin binciken man fetur mai suna Liaohe suka kafa cikin hadin guiwarsu, ya zuba jari da yawansu ya kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 2 musamman domin binciken na'urorin hakon man fetur da kuma kera su. Malam Hu Dexiang, babban manaja na babban kamfanin nan ya bayyana cewa, a sakamakon kyakkyawan yanayin zuba jari, kamfaninsa ya sami bunkasuwa cikin sauri a yankin raya tattalin arziki na Panjin. A cikin shekarun nan biyu da suka wuce bayan da aka kafa shi, yawan kudi da kamfaninsa ya samu wajen samar da kayayyaki ya kai kudin Sin Yuan miliyan 800, wato ke nan ya karu da ninki 5 bisa na farkon lokacin kafuwarsa. Yanzu kamfanin ya riga ya fitar da kayayyakinsa zuwa kasashe da shiyyoyi sama da 40 na nahiyoyin Amurka da na Turai da gabas ta tsakiya da tsakiyar Asiya da kudu maso gabashin Asiya.

1 2