Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-22 20:41:32    
Tabki mafi girma a kasar Sin

cri

Tabkin "Qinghai" yana da fadin muraba'in kilomita 4,583, kuma matsakaicin zurfinsa ya wuce mita 18. Kasancewar tabkin a kan plato, tsayin tabkin ya kai mita 3260 daga leburin teku, kuma yanayin wurin na da nishadi, ko a lokacin zafi ma ba a jin zafi sosai.

Kasancewar tabkin Qinghai a arewa maso gabashin platon Qinghai, a nan wurin, akwai makamakan filayen ciyayi, akwai kuma koguna masu dimbin yawa. Bayan haka, akwai kuma manyan duwatsu hudu da ke zaune a kewayen tabkin Qinghai.

Tabkin Qinghai ya yi suna ne sabo da albarkatun kifaye da yake da shi. Musamman ma wani irin kifin da ake kira "Huang". Da lokacin dari ya yi, bayan da tabkin Qinghai ya daskare, a kan hako kankarar da ke kan tabki, don kamun kifayen da ke cikinsa.

Bayan haka, a yammacin tabkin Qinghai, akwai wani tsibirin da ake kiransa "tsibirin tsuntsaye", wanda ya shahara kwarai da gaske sabo da dimbin tsuntsayen da ke zama a nan. Ko da yake wannan dan karamin tsibirin na da fadin mubara'in kilomita 0.8 kawai, amma tsuntsayen da suke yada zango a nan sun kai har dubu 100. A lokacin da aka sa kafa a kan tsibirin, ba shakka, tsuntsaye iri iri za su burge jama'a kwarai da gaske. Bayan haka, ko ina ana iya ganin kwayayen tsuntsaye iri iri. Domin ba da kariya ga tsuntsayen da ke tsibirin, an kuma kafa hukumar musamman a nan, don nazarin tsuntsayen da kuma kare su.

Bisa binciken da aka gudanar, an kuma gano albarkatun ma'adinai a cikin tabkin Qinghai.

Isashen ruwan sama da a kan samu a tabkin Qinghai a duk shekara ya samar da sharuda masu kyau ga bunkasa sana'ar kiwo da aikin gona. A gabar tabkin kuma, akwai makamakan makiyayai, inda ake kiwon dawaki da shannu da kuma tumaki, tun lokacin gargajiya, kyawawan dawakin da aka fitar daga nan wurin sun yi suna sosai. Ban da kiwon dabbobi, jama'ar wurin suna kuma kokarin bunkasa aikin gona, kuma filayen gona masu albarka sun tabbatar da kyakkyawan makomar aikin gona a wurin.

A gabar tabkin Qinghai, 'yan kabilun Han da Tibet da Mongoliya da dai sauran kabilu daban daban suna zaman rayuwarsu cikin jin dadi, kuma suna zaman jituwa da juna, suna kuma kokarin kiyaye wannan kyakkyawan tabki cikin hadin gwiwa.

Yanzu kyakkyawan yanayin tabkin Qinghai yana ta janyo masu yawon shakatawa daga gida da kuma waje, tabkin Qinghai ya riga ya zama wani shahararren wurin shakatawa na kasar Sin. Masu sauraro, idan kun sami damar zuwa kasar Sin a wata rana, kada dai ku wuce wannan kyakkyawan tabki na Qinghai.(Lubabatu)


1 2