

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Salihu Babangida, mazaunin birnin Jos da ke jihar Plato, tarayyar Nijeriya. Malam Salihu Babangida ya turo mana sakonsa a kwanan baya cewa, shin wane tabki ne ya fi girma a kasar Sin, ina so ku ba ni bayani a kan tabki din.
Tabkin Qinghai shi ya kasance tabki mafi girma a kasar Sin, haka kuma tabki mai ruwan gishiri mafi girma a kasar. Domin amsa tambayar malam Salihu Babangida, bari in kai ku wannan kyakkyawan tabki na kasar Sin.
Tabkin Qinghai wani kyakkyawan lu'u lu'u ne da ke kan platon Qinghai na kasar Sin, 'yan kabilar Tibet suna kiran tabkin da sunan "Cuowenbo", wanda ke da ma'anar "koren tabki", sa'an nan, a cikin harshen 'yan kabilar Mongoliya, sunan tabkin shi ne "Kukunuoer", wato "teku mai launin shudi".
1 2
|