Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-21 18:08:38    
Ministan harkokin na kasar Faransa ya yi a Iraki domin kokarin kyautata huldar da ke tsakanin Faransa da Amurka

cri

Haka kuma, manazarta sun bayyana cewa, Mr. Kouchner ya kai wa kasar Iraki ziyara ba domin muhimmiyar tattaunawar da aka yi a tsakanin Sarkozy da Bush kawai ba, har ma domin shugaba Sarkozy na kasar Faransa yana kokarin kyautata huldar da ke tsakanin Faransa da Amurka bayan da ya hau kan mukamin shugaban kasar. Sun nuna cewa, domin tsohon shugaban kasar Faransa Jacques Chirac ya kan yi suka da kakkausar harshe kan kasar Amurka domin ta ta da yakin Iraki, huldar da ke tsakanin Faransa da Amurka ta shiga mawuyacin hali. Amma Mr. Sarkozy mutum ne da ke amincewa da kasar Amurka. A ganinsa, rashin aminci a tsakanin Faransa da Amurka yana bata moriyar kasar Faransa. Ban da wannan, kasashen Faransa da Amurka muhimmin kasashen abokan cinikayya ne. Sabo da haka, kyautata huldar da ke tsakanin kasashen biyu abu ne da ya wajaba. Sakamakon haka, bayan da ya hau kan mukamin shugaban kasar Faransa, lokacin da yake tattaunawa da Mr. Bush ta hanyar waya, Mr. Sarkozy ya ce, "kasar Amurka za ta iya amincewa da zumunci daga wajen kasar Faransa", "Zumunci yana bayyana cewa abokai za su iya yin nazari kan batutuwa iri daban-dban ta hanyoyi daban-daban." A bayyane ne, wadannan maganganun da ya yi sun bayyana fatansa na kyautata huldar da ke tsakanin Faransa da Amurka.

Amma, a waje daya, manazarta sun nuna cewa, kasar Faransa ba za ta bi sawun kasar Amurka a kan dukkan batutuwa ba. Alal misali, a bayyane ne Mr. Sarkozy ya taba bayyana cewa ba ya yarda da a bunkasa kungiyar Nato fiye da shirin da aka tsara, kuma bai yarda da kungiyar Nato ta yi takara da M.D.D. ba. A kan batun sauyin yanayin duniya, Mr. Sarkozy ya nemi kasar Amurka da ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta kamar yadda ya kamata ta dauka. A kan batun nukiliya na kasar Iran, ya ce bai amince da shirin yin makaman nukiliya na Iran ba, ya kamata kasashen duniya su sanya takunkumi kan kasar Iran ba tare da kasala ba, amma bai yarda da a dauki matakin soja kan kasar Iran ba. Wannan matsayin da Mr. Sarkozy ke dauka ya bayyana cewa, zai ci gaba da tsaya tsayin daka kan matsayin da kasar Faransa take dauka a kullum kan muhimman batutuwan duniya. Yana kokarin daidaita huldar da ke tsakanin Faransa da Amurka ne bisa wannan tushe. (Sanusi Chen)


1 2