Ran 20 ga wata, rana ta biyu ce da ministan harkokin waje na kasar Faransa Bernard Kouchner yake ziyara a kasar Iraki. A wannan rana, kafofin watsa labaru na kasar Faransa sun bayar da sharhi bi da bi, inda suka nuna cewa, ziyarar da Mr. Kouchner ke yi a Iraki ziyarar farko ce da muhimmin jami'in gwamnatin kasar Faransa ya kai wa kasar Iraki tun bayan aukuwar yakin Iraki a shekarar 2003. Wannan ya ya yi nuni da cewa, hukumar Faransa tana mai da hankali sosai kan batun Iraki, yana kuma almantar da cewa, huldar da ke tsakanin Faransa da Amurka za ta kara samun kyautatuwa. A waje daya, wannan ziyara tana da nasaba da kyautatuwar huldar da ke tsakanin Faransa da Amurka bayan Mr. Nicolas Sarkozy ya hau kan mukamin shugaban kasar Faransa.
A ran 19 ga wata ne Mr. Bernard Kouchner ya isa kasar Iraki ya fara ziyarar aiki a kasar. Kafin ya tashi daga kasar Faransa zuwa kasar Iraki, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Faransa ya taba bayyana cewa, Mr. Kouchner ya kai wa kasar Iraki ziyara ne bisa gayyatar da shugaba Jalal Talabani na kasar Iraki ya yi masa. Yana son bayyana wa jama'ar kasar Iraki cewa, kasar Faransa tana hada kan kasar Iraki, kuma tana son sauraran ra'ayoyi daga wajen kungiyoyi daban-daban na Iraki.
Wannan kakaki ya kuma bayyana cewa, dalilin da ya sa Mr. Kouchner ya zabi ran 19 ga wata ya kai wa kasar Iraki ziyara shi ne, ba domin a wannan rana ne shugaba Sarkozy ya kawo karshen hutunsa a kasar Amurka ba, domin wannan rana ce ta cika shekaru 4 da mutuwar amininsa Sergio de Mello, wakilin musamman na M.D.D. kan batun Iraki sakamakon fashewar boma-bomai da aka yi a Bagadaza. Mr. Kouchner yana son nuna ta'aziyya ga Sergio de Mello a Bagadaza a wannan rana. Amma wasu manazarta ba su amince da wannan magana ba, sun nuna cewa, ziyarar da Mr. Kouchner ke yi a kasar Iraki tana da nasaba da hutun da shugaba Sarkozy ya yi a kasar Amurka kuma ya kawo karshen wannan hutunsa a wannan rana. Sun ce, tabbas ne Mr. Kouchner ya samu goyon baya daga wajen shugaban kasar wajen kai wa kasar Iraki ziyara ba zato ba tsammani. Sun nuna cewa, matsayin da Mr. Sarkozy ke dauka kuma ya nuna wa shugaba George W. Bush na kasar Amurka lokacin da suke ganawa da juna lokacin da Mr. Sarkozy ke hutu a kasar Amurka ya sasauta halin adawa da juna da ake ciki kan batun Iraki a tsakanin Faransa da Amurka har na tsawon shekaru 4, wannan tushe ne da ya sa kaimi kan ministan harkokin waje na kasar Faransa da ya kai ziyarar aiki a kasar Iraki a karo na farko a cikin shekaru 4 da suka wuce. A wannan rana, lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Iraki, Mr. Kouchner ya bayyana cewa, kasar Faransa tana son taimakawa kasar Iraki wajen tabbatar da kwanciyar hankali a kasar.
1 2
|