Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-21 17:17:06    
Hamadar Badanjilin da ke jihar Mongolia ta Gida a kasar Sin

cri

Malam Cai ya kara da cewa, wani abu mai ban mamaki daban da aka samu a hamadar Badanjilin shi ne karar da rairayi ke fitowa da ita a yayin da iska ta busa ta. Damshin iska da zafin yanayi da kuma canjin saurin iska da kuma bambancin muhalli sun zama sanadiyyar canje-canjen karar da rairayi ke fitowa. Wani lokaci, irin karar na da dadin ji, amma a wani lokaci, ya kan sa mutane fargaba. A matsayin kwararre mai ilmin yin kasada, amma a lokacin da malam Cai ya ji karar da rairayi ke fitowa da ita a karo na farko, ya firgice, ya ce, 'A lokacin da muke sauka daga wani babban tudun rairayi mai tsawo, ba zato ba tsammani, mun ji kara a karkashin kafafunmu. A lokacin can, mun ji mamaki. Jim kadan mun gano cewa, ita ce karar da rairayi ke fitawa. Babbar kara da rairayi ke fitowa a karkashin kafafunmu ta ba mu tsoro kadan. '

A hamadar Bajindalin mai fadi, wasu manyan duwatsun rairayi suna kewayen wani gidan ibada mai suna Badanjilin, shi ne gidan ibada kacal a wannan hamada. Ko da yake yana karami, amma darajar ginin da kuma kayayyakin gargajiya da aka samu a wajen sun yi daidai da wadanda aka samu a wasu manyan gidajen ibada. An kafa wannan gidan ibada a shekarar 1868, saboda yana karkara a hamadar, kuma ba safai mutane su kan kai masa ziyara ba, shi ya sa yana kasancewa kamar yadda yake a da, bai gamu da barna ba. Sa'an nan kuma, masu bin addinin Buddha da yawa ba su ji gajiyar doguwar tafiya ba, suna ta tafiya domin yin addu'a

Tabkuna da marmaron ruwa a hamadar Badanjilin su ma su kan ba mutane mamaki sosai. Akwai tabkuna 113 a hamadar. Abu mai ban mamaki shi ne a gabobin wadannan tabkuna masu ruwan gishiri ko kuma a cibiyoyinsu, a kan samu idanun ruwa manya da kanana, ruwan da ke fitowa daga wajen na da matukar zaki, ya sha bamban kwarai da ruwan gishiri da ake samu a tabkunan.

Ruwa ta yi sanadiyar rayuka a hamada. A hamadar Badanjilin, tabbas ne za ku ga mutane suna zaune a kusa da tabkuna. Iyalai 30 ko fiye sun yi shekara da shekaru suna zama a hamadar. Malam Chagankou, wani makiyayi a wannan hamada. Gidansa na dab da wani karamin tabki, shi ne kuma gida kacal a wuri mai fadin kilomita da dama. Chagankou ya bayyana cewa, ''Yan kauyanmu muna kiwon rakuma da tumaki a dausayi, ban da wannan kuma, kauyenmu yana da tabkuna da yawa, wani iyali na zama a dab da wani tabki, shi ya sa a dab da tabkuna fiye da 30, iyalai fiye da 30 suna zama a wajen, wato ke nan mutane fiye da dari 1 suna zama a nan.'

Ya zuwa yanzu, mazauna hamadar Badanjilin suna shakar iskar da ba a taba gurbata ta ba, suna shan ruwa mai tsabta da suka debo daga marmaron ruwa, suna cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu daga lambunansu, wadanda ba a taba gurbata su ba, sa'an nan kuma, suna rayuwa cikin kwanciyar hankali.


1 2