Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-21 17:17:06    
Hamadar Badanjilin da ke jihar Mongolia ta Gida a kasar Sin

cri

Hamadar Badanjilin tana arewacin gundumar Alashan da ke jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin, fadinta ya kai misalin murabba'in kilomita dubu 47, ta zama ta hudu a duk duniya saboda girmanta, haka kuma girmanta ya zama na uku a kasar Sin. A hamadar Badanjilin, wakilinmu ya gamu da wata budurwa mai suna Mier, wadda ke ziyara a wajen. Mier ta sha yin kasada a hamada, amma a karo na farko ne ta kawo wa hamadar Badanjilin ziyara. Game da kyan karkara a wajen, bakin Mier cike yake da matukar yabo, ta ce, 'In dare ya yi duhu, sai ana ganin launuka irin na bakan gizo a wurin da sararin sama da hamadar suka hade da juna. Yana da kyan gani sosai. Na dauki wasu hotuna a wajen, dukkansu na da matukar kyan gani.'

Manyan duwatsun rairayi da aka samu a hamadar Badanjilin kyan karkara ne da ke fi nuna sigar musamman a wajen. A sakamakon iska mai karfi har na tsawon shekara da shekaru, rairayi suna ta tafiya sun taru har ma sun fito da manyan duwatsun rairayi. A cibiyar hamadar, manyan duwatsun rairayi sun yi kama da babbar igiyar ruwa, a ciki kuma babban dutsen Bitulu ya fi tsayi, tsayinsa ya kai misalin mita dari 5 daga leburin teku, shi ne kuma babban dutsen rairayi mafi tsayi a kasar Sin har ma a duk duniya, ana kiransa babban tsaunin Everest a hamada. Malam Cai Nan, shugaban wani kulob din yin kundun bala a daji, ya taba jagorancin tim dinsa sun isa kololuwar wannan babban dutsen rairayi. A lokacin da yake bayyana ra'ayinsa kan hawan babban dutsen rairayin Bitulu, ya ce, 'Ana kiran babban dutsen Bitulu babban tsaunin Everest a hamada, shi ne kololuwa mafi tsayi a cikin dukkan hamada a duniya. Isa kololuwarsa ya yi kama da isa kololuwar wani babban tsaunin Everest daban. A yayin da muke hawan wannan babban dutse, a wani lokaci, mun yi amfani da hannu da kafa tare, mun taka zuwa gaba amma tare da komawa baya kadan.'

1 2