Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-20 20:45:08    
Likitocin yankin Taiwan ya yi aikin jiyya a birnin Fuzhou

cri

Wadannan likitoci 8 na asibitin Meidesheng sun zo daga biranen Taibei da Xinzhu da kuma Taizhong na yankin Taiwan, kuma sun nuna kwarewa a fannonin aikin jiyya na yara da mata da cikin jikin dan Adam da kuma tsoffi, kuma sun taba gudanar da wannan aiki cikin dogon lokaci a Taiwan. Cai Shunhui, daya daga cikinsu ya gaya wa wakilinmu cewa, "ana iya samun 'yan uwa na Taiwan masu yawa da suke aiki a birnin, lokacin da suke fama da cututtuka, sun fi son ganin likita daga wajenmu. Yanzu wani halin musamman na asibitinmu shi ne muna iya samar da muhalli mai kyau wajen ganin likita."

Cai Lianzhen, shugaban asibitin Meidesheng kuma wani likitan Taiwan ya bayyana cewa, bayan da aka kaddamar da ayyukan asibitin, mutane fiye da goma da ke fama da cututtuka sun zo wurin don ganin likita a ko wace rana, a ciki, yawancinsu 'yan uwa na Taiwan ne, har ma wasu daga cikinsu sun zo asibitin ne domin yin hira da likitocin Taiwan kawai a maimakon ganin likita. Kuma Mr. Cai ya kara da cewa, "sabo da bangarori biyu da ke tsakanin gabobin mashigin tekun Taiwan wato babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan na Sin suna ta kara yin cudanya tsakaninsu a fannoni daban daban, ciki har da ayyukan da ke da nasaba da aikin jiyya, shi ya sa aka ba mu wata dama wajen kafa wani asibiti a babban yankin kasar Sin. 'Yan kasuwa na Taiwan da yawa su ma sun kara kwarin gwiwarmu, cewa idan mun kafa wata hukumar jiyya, to za su samu taimako sosai daga wajenmu."

Tare da bunkasuwar dangantakar cinikayya tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, yawan 'yan kasuwa na Taiwan da suka zuba jari da kuma zama a babban yankin Sin da kuma iyalansu yana ta karuwa. Ana iya samun 'yan uwa na Taiwan kusan dubu 20 a cikin birnin Fuzhou. Amma sabo da akwai bambanci tsakanin asibitocin gabobin biyu wajen tabbatar da cututtuka da shan magunguna, shi ya sa idan 'yan kasuwa na Taiwan sun kamu da cututtuka marasa tsanani, kullum su kan sha magunguna a gida, amma idan sun kamu da cututtuka masu tsanani, su kan koma Taiwan don ganin likita. Yanzu likitocin Taiwan sun kaddamar da aikinsu a birnin Fuzhou, wannan ya ba da sauki sosai gare su. Chen Bo'an, wani dan uwa na Taiwan da ya zo asibitin Meidesheng don ganin likita ya gaya mana cewa, "dalilin da ya sa na zo asibitin shi ne sabo da na saba da likitocin Taiwan. Lokacin da na zo asibitin, na kan ji annashuwa."

Mr. Cai, shugaban asibitin ya kuma bayyana cewa, yanzu asibitin Meidesheng asibiti ne da yake da likitocin Taiwan mafi yawa a duk lardin Fujian, ba kawai asibitin yana iya yin jiyya kan yara da cikin jikin dan Adam da kuma baka ba, har ma yana hadin gwiwa tare da asibitin hukumomin gwamnatin lardin Fujian, ta yadda za a iya yin amfani da manyan kayayykin binciken lafiyar jiki tare, da kuma kaura da mutanen da ke fama da cututtuka masu tsanani zuwa asibitin. Game wannan, Ji Xiaolin, shugaban asibitin hukumomin gwamnatin lardin ya bayyana cewa, "bayan da aka tafiyar da wannan aiki, muna iya bayar da gudummowa ga 'yan uwa na Taiwan da ke zama a babban yankin kasar Sin a fannin jiyya. Muna fatan za mu iya ci gaba da hadin kanmu a nan gaba domin bauta wa mutanen da ke fama da cututtuka."

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin ke nan. Muna fatan kun ji dadinsu, da haka a madadin Kande wadda ke fassara bayanin, Lawal nake cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)


1 2