Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-20 20:45:08    
Likitocin yankin Taiwan ya yi aikin jiyya a birnin Fuzhou

cri

A kwanan nan, likitoci 8 na yankin Taiwan na kasar Sin sun je birnin Fuzhou, wani birni ne da ke bakin teku da ke kudu maso gabashin kasar Sin domin kaddamar da aikin jiyya, wannan shi ne karo na farko da likitocin yankin Taiwan suka yi aikin jiyya bayan da suka samu iznin yin aikin cikin dan lokaci kadan a lardin Fujian na kasar Sin. Kuma wannan matakin da ake dauka ya kawo wa mazaunan birnin Fuzhou alheri sosai, musamman ma ya samu karbuwa sosai daga 'yan uwa na Taiwan da ke birnin. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu leka wannna asibiti mai suna "Meidesheng".

Shigowar wakilinmu cikin kofar asibitin ke da wuya, sai nas mai ja gora ta zo da hannu biyu biyu. A cikin asibitin, ana iya ganin wata taswirar ja-gora a kan bango na gefen hagu, kuma hotunan likitocin Taiwan 8 da na sauran likitoci a kan bango na dama. A hawa na biyu kuma kofofi da tagogi suna da tsabata sosai, haka kuma akwai wani dakin shan kofi da ke da kyakkyawan muhalli don hutawa.

An mai da hankali sosai kan wadannan likitoci 8 da suka zo birnin Fuzhou daga yankin Taiwan, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da su likitocin Taiwan na rukunin farko ne da ke samun iznin yin aikin jiyya cikin gajeren lokaci a lardin Fujian bayan da babban yankin kasar Sin ya dauki matakin da abin ya shafa, wato an amince da likitoci 'yan uwa na Taiwan masu cancanta wajen yin rajista da kuma kaddamar da aikinsu a babban yankin kasar Sin.

1 2