Malam Zhang ya yi bayani kan wannan cewa,'Yankin arewa maso gabashin kasar Sin yanki ne da ake samun albarkatun halittu masu kyau, shi ne kuma muhimmin sansanin kasarmu wajen samar da hatsi da kuma muhimmin wurin da aka dasa bishiyoyi. Sa'an nan kuma, ana samun gandun daji masu fadi a wajen, shi ya sa yankin yana taka muhimmiyar rawa a fannin kiyaye tsarin muhallin halittu saboda ana shuka bishiyoyi da ciyayi da yawa a wajen. Saboda haka, ya zama wajibi gwamnatin Sin ta dora muhimmanci kwarai kan kiyaye kasa mai cike da taki da kuma albarkatun gandun daji a arewa maso gabashin kasar Sin.'
Malam Zhang ya kara da cewa, baya ga kara shuka bishiyoyi, gwamnatin Sin za ta dauki matakai domin hana sare bishiyoyin halittu don kiyaye albarkatun bishiyoyin halittu masu daraja a arewa maso gabashin kasar Sin. A sa'i daya kuma, gwamnatin Sin za ta sa kaimi kan raya masana'antun noma laiman kwadi da sauran irinsa da kuma kiwon wasu namun daji.
Dadin dadawa kuma, malam Zhang ya ci gaba da cewa, a yayin da take aiwatar da shirin farfado da arewa maso gabashinta, kasar Sin za ta mai da hankali sosai kan sa kaimi kan bude kofar wannan yanki ga kasashen duniya, za ta karfafa gwiwar kasashen waje da su zuba jari kan masana'antun fasahohin zamani da na kera injuna da kuma kiyaye muhalli da dai sauransu. Ban da wannan kuma, a cikin muhimman biranen da ke bakin iyakar kasa, za ta gaggauta kafa shiyyoyin hadin kan tattalin arziki da shiyyoyin ciniki na birane da shiyyoyin raya masana'antu a ketare kasa da kasa. Amma duk da haka, kasar Sin za ta kayyade ko kuma hana baki 'yan kasuwa su zuba jari kan masana'antun da ke fi bata makamashi, suke kuma fi gurbata muhalli.(Tasallah) 1 2
|