Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-20 18:33:03    
Kasar Sin tana mai da hankali kan kyautata tsarin muhallin halittu da kiyaye muhalli wajen farfado da arewa maso gabashinta

cri

A ran 20 ga wata, a nan Beijing, a gun taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, malam Zhang Guobao, darektan ofishin jagorancin ayyukan farfado da tsoffin sansanonin masana'antu da suka hada da yankin arewa maso gabashin kasar Sin kuma mataimakin darektan kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin, ya nuna cewa, a cikin shirin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin da aka fito da shi a kwanan baya, an tabbatar da cewa, za a yi shekaru 10 zuwa 15 domin raya yankin arewa maso gabashin kasar Sin zuwa wani muhimmin yanki mai ci gaban tattalin arziki. Ya ce,'Makasudin da aka tanada a cikin wannan shiri shi ne neman raya yankin arewa maso gabashin kasar Sin zuwa sansanin kera injuna wadanda za su iya takara a ko ina a duniya, da sansanin kasar wajen ba da tabbacin sabbin danyun kayayyaki da makamashi, da muhimmin sansanin samar da hatsi da ayyukan gona da kiwon dabbobi, da kuma muhimmin sansanin kasar a fannin nazari da sabunta fasahohi.'

Yankin arewa maso gabashin kasar Sin ya hada da lardunan Heilongjiang da Jilin da Liaoning. An taba dasa harsashi mai inganci ta fuskar masana'antu a wajen, ana samun dimbin albarkatun man fetur da kwal da karfe da dai sauransu a nan, haka kuma yankin na taka muhimmiyar rawa wajen samar da hatsi. Amma tun bayan shekarun 1980 har zuwa yanzu, saboda dalilai da yawa, bambancin da ke tsakanin wannan yanki da yankunan kasar Sin masu ci gaba da ke bakin teku a fannin bunkasuwar tattalin arziki yana ta karuwa.

A shekarar 2003, kasar Sin ta soma aiwatar da muhimman tsare-tsaren farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin. Ko da yake wannan yanki ya sami ci gaba, amma yana fuskantar wasu matsaloli. Kasar Sin na matukar bukatar rarraba ayyukan raya wannan yanki.

A cikin irin wannan yanayi ne, gwamnatin Sin ta fito da 'shirin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin'. A cikin wannan shiri, an mai da hankali sosai kan kyautata tsarin muhallin halittu da kiyaye muhalli a arewa maso gabashin kasar Sin, an kuma fito da makasudai da yawa domin kyautata muhallin halittu.

1 2