Da aka tabo magana a kan sauye-sauye da jihar Tibet ta samu daga wajen hanyar jirgin kasar, sai aka yi magana a kan harkokin yawon shakatawa. Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin ta yi, an ce, tun daga watan Janairu zuwa watan Mayu na bana, yawan masu yawon shakatawa da jihar ta karba da kuma yawan kudin da jihar ta samu daga wajen harkokin yawan shakatawa duk ya karu da kashi 30 cikin dari ko fiye bisa na makamancin lokaci na bara. Masu yawon shakatawa wadanda ke zuwa jihar Tibet suna more idanunsu ni'imatattun wurare da ke kan duwatsun Tibet, kuma suna kara yadada al'adun gargajiya na kabilar Tibet zuwa wurare daban daban.
Yayin da ake samun taimako daga wajen hanyar jirgin kasa ta Qinghai da Tibet wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar Tibet, ko da yaushe kasar Sin tana mai da hankali sosai ga kiyaye yanayin kasa a duwatsun Tibet. Malam Zhang Yongze, shugaban hukumar kiyaye muhalli ta jihar Tibet ya bayyana cewa, jihar ta riga ta dauki tsaurarran matakai wajen kiyaye muhalli don daidaita batun gurbacewar muhalli da za a gamu da shi bayan kaddamar da hanyar jirgin kasa ta Qinghai da Tibet. Ya bayyana cewa, "kafin a kaddamar da hanyar jigirn kasa ta Qinghai da Tibet, mun riga mun yi bincike a kan batun gurbacewar muhalli da zai wakana bayan fara aiki da hanyar, da kuma matakai da za mu dauka don magance batun. Haka kuma bisa ci gaba da za a samu wajen bunkasa aikin masana'antu da harkokin yawon shakatawa ta hanyar kaddamar da hanyar jirgin kasar, mun bukaci kamfanonin da suka gina hanyar da su mai da hankali sosai ga kiyaye muhalli tun lokacin da suka fara tsara fasalin hanyar. " (Halilu) 1 2
|