A ran 1 ga watan Yuli na shekarar bara, an kaddamar da duk hanyar jirgin kasa ta Qinghai da Tibet, wadda ita ce hanyar jirgin kasa mafi tsawo a kan duwatsu mafi tsayi a duniya, ta haka an kawo karshen tarihin rashin samun hanyar jirgin kasa a jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin. A cikin shekara daya da ta wuce, wannan hanyar jirgin kasa ta ba da babban taimako wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar.
Da malam Nimaciren, mataimakin shugaban gwamnatin jihar Tibet ya tabo magana a kan hanyar jirgin kasar, sai ya bayyana cewa, "ana aiki da hanyar jirgin kasa ta Qinghai da Tibet da kyau a cikin kusan shekara 1 da ta wuce. Sabo da haka ina wa kasarmu godiya sabo da an kawo karshen tarihin rashin samun hanyar jirgin kasa a jihar Tibet. Ya kamata, a ce, wannan yana da muhimmanci sosai ga canja aikin samar da kayayyaki da zaman rayuwa a jihar Tibet."
Ana samun taimako daga wajen hanyar jirgin kasar wajen bunkasa harkokin sufurin kayayyaki a jihar Tibet. A watan Yuli da ya wuce, ta hanyar jirgin kasar, jihar Tibet ta fara jigilar ruwan sha mai inganci da ake samu daga kankara da ke kan duwatsu masu tsayin mita 5,100 daga leburin teku zuwa wurare daban daban na duniya. Madam Jiang Xiaohong, babbar manaja ta babban kamfanin samar da ruwan sha iri na kankarar Tibet na 5100 ta bayyana cewa, wani babban dalilin da ya sa kamfaninta yake aiwatar da harkokin samar da ruwan nan, shi ne domin kaddamar da hanyar jirgin kasa a Tibet. Ta kara da cewa, "kafin kamfaninmu ya gina gidan ruwan sha irin na kankarar Tibet, an riga an fara shimfida hanyar jirgin kasa ta Qinghai da Tibet. Bayan da muka sami labarin, mun fara aikin gina gidan ruwan. Bayan da aka yi zirga-zirgar jirgin kasar a cikin shekara daya da ta wuce, an tabbatar da cewa, kudurin kan gina gidan ruwanmu daidai ne. "
Bayan da aka kaddamar da hanyar jirgin kasa ta Qinghai da Tibet, mun rage yawan kudi da muke kashewa wajen jigilar kayayyakinmu zuwa wurare daban daban na gida da waje, ta haka mun kara samun karfi wajen yin takara a kasuwanni.
1 2
|