Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-10 17:50:46    
Ana samu fa'ida mai yawa wajen yin aikin noma ta hanyar tsimin ruwa.

cri

Ban da ana kara yadada fasahar shayad da gonaki ta hanyar zamani a kauyuka da yawa na kasar Sin, kuma ana bin sabbin hanyoyi wajen kula da albarkatun ruwa bisa gwaji. Alal misali a kauye mai suna Jiamakou na lardin Shanxi, ana bin wata sabuwar hanya wajen kula da albarkatun ruwa a fili, wato wata kungiyar kula da albarkatun ruwa da manoman kauyen suka zaba tana kula da harkokin rarraba ruwa ga manoma, kuma ta kan bayyana musu farashin ruwa da yawan ruwa da aka yi amfani da kuma lokacin samar da ruwa da sauransu cikin lokaci-lokaci a fili. Ta haka an kara ba da kwarin giuwa ga monoma da su shayad da gonakinsu ta hanyar tsimin ruwa.

Yanzu, yawan filayen gonaki da ake shayad da su ta hanyar tsimin ruwa ya karu, amma ya zuwa yanzu dai matsala mai tsanani da ake fuskanta ita ce karancin kudi. Malam Li Yuanhua, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin tsare ruwa na kauyuka na ma'aikatar tsare ruwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "a kasar Sin, matsakaicin filin gonaki na ko wane manomi na kasar Sin ya yi kadan, kuma manoma suna aikin gona cikin iyali, don haka manoma ba su iya kashe makudan kudade wajen kyautata aikin shayad da gonaki ta hanyar tsimin ruwa ba, Ka zalika ba a iya dogara da iyalan manoma ko wani kauye wajen yin aikin noma ta hanyar tsimin ruwa ba."

Malam Li Yuanhua ya kara da cewa, ma'aikatarsa za ta yi kokari wajen sa kaimi ga bangarorin jama'a daban daban da su zuba jari wajen kawar da karancin ruwa mai tsanani da ake yi a manyan wuraren noma hatsi, da gudanar da tsimin ruwa a wurare da ake fama da talauci, kuma za ta sa kaimi ga manoma da su shayad da gonaki ta hanyar zamani don tsimin ruwa. (Halilu)


1 2