Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-10 17:50:46    
Ana samu fa'ida mai yawa wajen yin aikin noma ta hanyar tsimin ruwa.

cri

Ruwa da ake amfani da shi wajen yin aikin noma ya fi yawa a kasar Sin, yawansa ya dauki kashi sama da 64 cikin dari bisa jimlar ruwa da ake amfani da shi a kasar Sin baki daya. Amma ba a karfafa amfani da ruwa sosai ba a kasar. A halin da ake ciki a kasar Sin dangane da karancin ruwa sosai, an fara yin aikin noma ta hanyar tsimin ruwa a wurare da yawa na kasar. A cikin dogon lokaci, a kan yi karancin ruwa a arewacin kasar Sin. Yanzu za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan yadda ake yin aikin noma ta hanyar tsimin ruwa a arewacin kasar Sin.

A kauye mai suna Dongliang na birnin Zhaoyuan na lardin Shandong na kasar Sin, tsoho Liu Xingliang mai shekaru 65 da haihuwa yana noman inabi a filin gonaki masu kadada sama da 30. Da shiga cikin lambunsa, za a ga bututun roba sirara birjik inda ruwa ke fitowa kadan kadan kuma sannu sannu don shayar da gonakinsa. Malam Liu Xingliang ya ce, yana yin aikin noma ta hanyar zamani don tsimin ruwa. Ya ce, "bai kamata a shayad da gonakin noman inabi da ruwa sosai ba, bishiyar inabi tana da manyan saiyoyi mai nisan centimita 20 a karkarshin kasa, a nan ne nake shayar da ita da taki da ruwa ta hanyar bututun roba sirara birjik, ta haka an shayad da gonakin noman inabi da isasshen ruwa, ina kara shiyad da su da ruwa a sauran wurare, ba amfani."

A kauyuka da yawa na arewacin kasar Sin, manoma sun canja tsire-tsire da suke noma don shayad da gonaki ta hanyar zamani. A wani kauye mai suna Dongnanfang ta lardin Shanxi, a da manoma sun kan yi noman dawa da masara, yawan kudi da suke samu daga wajen sayar da hatsin nan a ko wace kadada ya kai kudin Sin Renminbi Yuan 13 kawai. Da malam Yang Shengli, dagacin kauyen ya gane cewa, ba a samu kudi mai yawa daga wajen hatsin da ake noma a gonaki masu fari ba, sai ya jagoranci manoman kauyensa wajen noman ciyayin dabbobi da bishiyoyi masu ba da 'ya'ya wadanda ba su bukatar ruwa mai yawa ba, sa'an nan sun fara ban ruwan gonakinsu ta hanyar tsimin ruwa. Dagaci Yang Shenli ya bayyana cewa, "ta haka, yawan kudin shiga da manomanmu suka samu daga wajen ciyayi da ya'yan itatuwa da suka noma ya karu sosai, wato yawan kudin da manoman ke samu wajen ciyayi da ya'yan itatuwa da suke noma a ko wace kadada ya karu da ninki 1.5 bisa na da. Yanzu, fadin gonaki da muke noman ciyayin dabbobi ya wuce kadada 130, kuma ana kula da su ta hanyar zamani. "

1 2