A gun ganawarsu, mataimakin shugaban kasar Iran Mr Parviz Davoudi ya yi alkawari cewa, Iran za ta ci gaba da taimakawa jama'ar Iraki da su samu gas mai dumama daki a lokacin sanyi. Mr Davoudi ya ci gaba da cewa, kasar Iran za ta kafa wata masana'antar tace mai a yankin Kerbala na kasar Iraki. Ban da wannan kuma, kasashen biyu na Iran da Iraki za su daddale wata yarjejeniya kan jigilar mai ta hanyar batutun man fetur, wadda ta tashi daga birnin Abadan da ke kudu maso yammacin kasar Iran, har zuwa birnin Basra na kasar Iraki. Ta wadannan batutunan man fetur, kasar Iran za ta iya shigar da man fetur daga Iraki, sa'an nan kuma, Iran za ta samar da kayayyakin mai ga jama'ar Iraki, domin tabbatar da biyan bukatunsu kan makamashi. Ban da wannan kuma, kasar Iran za ta bayar da rancen kudi da yawansu zai kai dalar Amurka biliyan guda, domin taimakawa Iraki da ta kyautata ayyukan masana'antu.
A lura cewa, a yayin da firayin minista Maliki yake ziyara a kasar Iran, an bude taron kwamitin hadin kai da shiga tsakani kan aikin tsaro na kasashen da ke makwabtaka da Iraki a ranar 8 ga wata a birnin Damascus, babban birnin kasar Sham, inda aka tattauna kan halin tsaro da ake ciki a Iraki, da kuma yadda ake samun zaman lafiya a iyakar kasa da ke tsakaninsu da Iraki. Wakilin Iran ya halarci wannan taro. Lallai, wannan ya nuna cewa, kasar Iran tana amfani da hanyarta, domin taimakawa Iraki da ta daidaita rikicin a gabanta.(Danladi) 1 2
|