Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-10 14:27:42    
Ziyarar firayin ministan kasar Iraki a Iran

cri

A ran 9 ga wata, firayin ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki ya kawo karshen ziyararsa ta yini biyu a kasar Iran, wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinta. A lokacin ziyararsa, bi da bi ne Mr Maliki ya gana da shugaban addini na kasar Iran Ali Khamenei, da shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad, da mataimakin shugaban kasar Mr Parviz Davoudi, da sakataren hukumar koli ta tsaron kasa Mr Ali Larijani, da kuma ministan harkokin waje na kasar Iran Mr Manouchehr Mottaki. A takaice dai, firayin ministan kasar Iraki Mr Maliki ya samu nasara daga ziyararsa a Iran. Sabo da ya samu goyon baya kan aikin tsaro da hadin kan tattalin arziki da kuma samar da makamashi da dai sauran abubuwan da ke jawo hankulan jama'ar Iraki.

Makasudi mafi muhimmanci na ziyarar Mr Maliki shi ne, domin neman cikakken goyon baya daga kasar Iran kan aikin tsaro, ta yadda za a iya sassauta tashin hankali da ake ciki a kasar Iraki a halin yanzu. A yayin da yake shawarwari da mataimakin shugaban kasar Mr Parviz Davoudi, Mr Maliki ya bayyana a fili cewa, dalilin da ya sa ya kai ziyara a kasar Iran a wannan karo shi ne, domin neman taimako daga kasar Iran, da kuma shawo kan kalubale da suke fuskanta tare.

Kasar Iran kuma ta nuna cewa, tana son taimakawa kasar Iraki kan sake gina kasa da maido da zaman karko a kasar. A yayin da mataimakin shugaban kasar Mr Parviz Davoudi yake ganawa da Mr Maliki, ya fadi cewa, har kullum kasar Iran tana dukufa wajen taimakawa Iraki ga kyautata halin tsaro da ake ciki a kasar, zaman lafiyar Iraki zai samar wa kasar Iran da duk shiyya alheri. Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad shi ma ya bayyana cewa, Iran da Iraki dukkansu suna da babban nauyi daya da ke bisa wuyansu na kiyaye zaman lafiya a shiyyarsu. A ganin Mr Ahmadinejad, makomar wannan shiyya ta danganci zaman lafiya da zaman karko a kasar Iraki.

Makasudi na biyu na ziyarar Mr Maliki a kasar Iran shi ne, domin kara raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu na Iraki da Iran, da kuma kara hadin kansu a fannonin daban daban, musamman a kan tattalin arziki.

1 2