Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-09 21:54:21    
Beijing na cike da imani don marabtar ranar cika shekara daya da ta rage da gudanar da taron wasannin Olympic

cri

" Taron wasannin Olympic ya kasance tamkar wani gagarumin biki ne da akan gudanar domin yayata hasashen Olympic da kuma samari na kasashe daban-daban wadanda suke da kyakkyawan burin shiga gasani masu ban sha'awa".

A albarkacin zagayowar ranar cika shekara daya da ta rage don gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing, Malam Wang Wei ya fada wa manema labaru cewa: " Gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympic na shekarar 2008 dake dake da sigar musamman, wani irin alkawari ne da muka dauka ga duk duniya; kuma kyakkyawan buri da bege ne na gwamnatinmu da jama'armu. A galibi dai, ana gudanar da ayyuka iri daban-daban na share fagen taron wasannin Olympic na Beijing lami-lafiya".

Wakilinmu ya ziyarci wani shahararren dan wasan gudu na gajeren zango daga kasar Amurka kuma tsohon zakaran taron wasannin Olympic, Carl Lewis, wanda ya fadi cewa: " Babu tantama, taron wasannin Olympic na Beijing zai zama wani taron wasanni mafi kyau a duniya".

Mr. Hain Verbruggen, shugaban kwamitin kula da harkokin taron wasannin Olympic na Beijing na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya yi farin ciki da fadin cewa: " Ya zuwa yanzu dai, an cimma nasara daga dukan bangarori wajen ayyukan share fagen wannan gagarumin taro. A kowane taron ganawa da manema labaru da akan shirya, akan nuna yabo sosai ga mahukuntan birnin Beijing".

Amma duk da haka, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing Mr. Jiang Xiaoyu ya furta cewa, lallai ya kasance da kalubale da za mu samu daga fannoni da dama, musamman ma a fannin muhallin hidimomi. Amma mun lashi takobin gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympic domin gamsar da jama'armu da na duk duniya. ( Sani Wang )


1 2