Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-09 21:54:21    
Beijing na cike da imani don marabtar ranar cika shekara daya da ta rage da gudanar da taron wasannin Olympic

cri

Aminai 'yan Afrika, ran 8 ga watan Agusta, rana ce ta cika shekara daya da ta rage don gudanar da bikin bude taron waannin Olympic na Beijing. Lallai wannan rana na da muhimmancin gaske ga birnin Beijing. A wannan rana, mutane masu yawan gaske na duniya sun yi wannan tambaya cewa shim ko Beijing ta shirya sosai wajen gudanar da taron wasannin Olympic shekarar 2008? To, yanzu sai ku saurari wani labarin da wakilanmu suka dauka a kan cewa ' Beijing na cike da imani wajen marabtar ranar cika shekara daya da ta rage don gudanar da taron waannin Olympic'.

Domin marabtar wannan rana mai ma'ana, an gudanar da jerin shagulgulan taya murna a ran 8 ga wata a wurare daban daban na kasar Sin. A birnin Beijing, dubun dubatar mazauna birnin Beijing sun yi wasannin motsa jiki a wannan rana da asuba a cikin lambunan shan iska da filaye kusan dubu daya na birnin don nuna goyon baya ga shirya taron wasannin Olympic a nan Beijing. Musamman ma wani irin halin annashuwa ya bullo a daren wannan rana a filin Tiananmen.

A daidai karfe 8 na dare ya yi da aka duba daga lambar kidayar yawan tsawon lokaci da ya yi saura don gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing da aka kafa a bakin filin Tiananmen, nan take mazauna birnin Beijing da kuma gaggan baki daga babban iyalin Olympic na kasa da kasa su fiye da 4,000 suka yi sowwa cikin fara'a. Daga baya, a wannan wuri ne shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, Jacques Rogge ya bada goron gayyatar kwamitocin wasannin Olympic daban-daban na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa don su turo 'yan wasa ga shiga taron wasannin Olympic na Beijing. A cikin jawabin da shugaba Rogge ya yi, ya buga take ga ayyukan share fagen taron wasanin Olympic na Beijing da ake yi; Kazalika ya yi kira ga samari matasan duk duniya da su zo nan Beijing domin yin nishadi.

1 2