Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-08 16:45:54    
Kasar Sin tana kara karfi ga kiyaye littattafan tarihi na zamani aru aru

cri

Kasar Sin tana kokarin raya tattalin arzikinta, a sa'I daya kuma a cikin 'yan shekarun da suka wuce, ta kara mai da hankali wajen kiyaye da yin gadon al'adun gargajiyarta. Kwanan baya ba da dadewa ba, ta kafa cibiyarta ta kiyaye littattafan tarihi na zamani aru-aru, wannan ne sabon matakin da kasar Sin ta dauka don kara inganta ayyukan kiyaye littattafan tarihi na zamani aru-auru. Kwararru sun kimanta cewa, bisa sabon matakin nan, za a iya kiyaye littattafan tarihi na zamani aru-aru wadanda suke bazuwa a wurare daban daban na kasar Sin .

Game da littattafan tarihi na zamani aru-aru, kasashe daban daban suna da ma'auninsu daban daban gare su. A kasar Sin, littattafan da aka buga su kafin shekarar 1911 ana kiransu da cewar littattafan tarihi na zamani aru-aru.

Gidan tanada littattafai na kasar Sin hukuma ce mafi girma da take tanadin littattafai mafi yawa a kasar. Yanzu yawan littattafan tarihi na zamani aru-aru da take tanade da su ya kai miliyoyi da yawa wadanda wasu daga cikinsu suke da tarihi da yawan shekarunsu ya wuce dubu. Ban da wannan gidan, wasu gidajen tanada littattafai na gundumomi da na larduna su ma suna tanadin littattafan tarihi na zamani aru-aru da yawa. Amma abin bakin ciki shi ne, a duk kasar Sin, ba a sami wani littafin da ya rubuta sunayen littattafan tarihi na zamani aru-aru ba

1 2