Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-08 16:45:54    
Kasar Sin tana kara karfi ga kiyaye littattafan tarihi na zamani aru aru

cri

Mr Li Zhizhong da ke da shekaru 70 da haihuwa wani mashahurin kwarrare mai kiyaye littattafan tarihi ne na zamani aru-aru na kasar Sin, ya yi nazari sosai a kan littattafan tarihi na zamani aru-aru iri daban daban masu yawa. A cikin 'yan shekaru da yawa da suka wuce, ya yi ta kira ga gwamnati da ta yi bincike kan littattafan tarihi na zamani aru-aru wadanda suke bazuwa a wurare daban daban na kasar Sin da kuma tsara dayantaccen ma'aunin kiyaye su, ya ce, wasu nagartattun litattattafan tarihi na zamani aru-aru suna yaduwa har zuwa yanzu, wannan ba abu ne mai sauki ba, saboda wasu an riga an lalata su sosai da sosai. Bayan bincike cikin dogon lokaci, sai ma'aikatar harkokin kudi da ma'aikatar al'adu ta kasar Sin suka dauki mataki don kiyaye wadannan littattafai masu daraja sosai.

Da aka shiga karni na 21, kasar Sin ta kara mai da hankali wajen kiyaye al'adun gargajiya, ta tattara littattafan tarihi da yawansu ya wuce dubu goma. A shekarar 2002, gwamnatin kasar Sin ta ware kudaden musamman don yin gyare-gyare kan wasu nagartattun littattafan tarihi. Wata shugaba mai kula da aikin nan mai suna Chen Hongyan ta bayyana cewa, a karo na farko, mun zabi wasu nagartattun littattafan tarihi don sake buga su da kuma gyara su, yanzu yawan ire-irensu ya kai 32, wadanda suka fito ne daga daular Tang, Son da Jin da Min da Qing da dai sauran dauloli, sauransu ana nan ana daukar hotunansu da gyara su da sake buga su.

Mun sami labari cewa, dukkan littattafan tarihi na zamani aru-aru sun sami cikas wajen kare ingancinsu bisa matakai daban daban, in ba a gyara su ba, to ba za a iya yin amfani da su ba, har ma ba za a iya daukar hotunansu ba. Wajen gyara su, ba za a iya yin amfani da sauran hanyoyi ba, sai ta hanyar yin amfani da hannun mutane kawai, saboda haka, za a kashe lokatai da yawa kuma sannu sannu sosai. A wani lokaci, in ana son gyara wani littafin tarihi na zamani aru-aru, dole ne a kashe lokutan da suka kai rabin shekara ko shekara daya, amma a kasar Sin, yanzu yawan kwararrun da suka iya gyara littattafan tarihi na zamani aru-aru bai wuce 100 ba, matsalar ta riga ta jawo hankalin sassan da abin ya shafa na kasar Sin.

Direktan cibiyar kiyaye littattafan tarihi na zamani aru-aru ta kasar Sin Mr Zhan Furui ya bayyana cewa, hanyar gyara littattafan tarihi na zamani aru-aru da ake yin amfani da ita yanzu a kasar Sin ba hanyar zamani ba, kuma kwararrun gyare-gyare ba su da yawa, ya ce, aikin nan aiki ne mai muhimmanci sosai, ya bayyana cewa, wannan yana da nasaba da batun gadon al'adun gargajiyar kasar Sin, kuma shi ne dawainiya mai nauyi sosai gare mu. Idan mun tattara littattafai da yawa, to za mu iya samun sakamako mai kyau wajen gadon al'adun gargajiyar kasar Sin, amma a wajen zuri'armu, idan muka sami cikas sosai wajen gadon al'adun gargajiya, to babbar matsala ce da muka samu wajen yada al'adun kasar Sin.(Halima)


1 2