Furofesa Williamson na jami'ar Sheffield ta kasar Birtaniya ya ce, sakamakon nazarin da muka yi ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne shan koren shayi zai ba da taimako wajen rage hadarin kamuwa da cutar kanjamau da kuma rage yaduwar kwayoyin cutar.
Amma a waje daya kuma ya jaddada cewa, shan koren shayi bai iya warkar da cutar kanjamau ba, haka kuma bai iya shawo kan cutar ba. Amma game da mutanen da suke fama da cutar kanjamau, shan koren shayi zai iya sassauta halin da suke ciki dangane da cuta.
Ban da wannan kuma furofesa Willanmson ya bayyana cewa, za a ci gaba da yin nazari kan cewa, ko yawan koren shayi da aka sha zai ba da tasiri ga sinadarin da ke cikinsa wajen hana kwayoyin cutar kanjamau ko a'a.
Ba kawai shan koren shayi zai ba da taimako wajen sassauta cutar kanjamau ba, har ma zai iya rage hadarin mutuwar mutane sakamakon toshewar jijiyoyin jini na kwakwalwa.
Bisa labarin da wani kamfanin dillancin labarai na kasar Japan ya bayar, an ce, manazarta masu ilmin kiwon lafiyar jama'a na jami'ar Tohoku ta kasar Japan sun gudanar da wani bincike tun shekara ta 1994 ga mutane fiye da dubu 40 da shekarunsu ya kai daga 40 zuwa 79 na haihuwa. Kuma manazarta sun kasa su cikin rukunoni hudu bisa yawan koren shayi da su kan sha.
Daga baya kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da wadanda su kan sha koren shayi yadda ya kamata, idan yawan karuwar koren shayi da suka sha, za su samu raguwar hadarin mutuwa sakamakon cututtukan kwakwalwa da zuciya. Hadarin mutuwar maza da su kan sha koren shayi na kofuna biyar a ko wace rana zai iya raguwa da kashi 22 cikin dari idan an kwatanta su da wadanda ba safai su kan sha koren shayi har kofi guda a ko wace rana ba. Haka kuma game da mata, irin wannan hadari zai ragu da kshi 31 cikin dari. A cikin hadarin mutuwar mutane sakamakon toshewar jijiyoyin jini na kwakwalwa ya samu raguwa a bayyane, wato zai ragu da kashi 42 cikin dari ga maza sa'an nan zai ragu da kashi 62 cikin dari ga mata. 1 2
|