Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-07 16:47:53    
Wani sinadarin da ke cikin koren shayi zai iya shawo kan kwayoyin cutar kanjamau

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, wani sinadarin da ke cikin koren shayi zai iya shawo kan kwayoyin cutar kanjamau, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan Xu Yirong, wani kwararren kasar Sin wajen shinkafa. To, yanzu ga bayanin.

Bayan da masu ilmin kimiyya na kasashen Birtaniya da Amurak suka gudanar da wani bincike, sun gano cewa, wani sinadarin da ke cikin koren shayi wato green tea zai iya hana kwayoyin cutar kanjamau su kasance a kan kwayoyi masu kare garkuwar jiki.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Birtaniya suka bayar a ran 31 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, an ce, manazarta sun gano cewa, koren shayi yana kunshe da wani sinadari mai suna EGCG, idan irin wannan sinadari ya kasance a kan kwayoyi masu kare garkuwar jiki da farko, to kwayoyin cutar kanjamau ba su da damar kasancewa a kansu.

1 2