Yanzu, bikin baje koli na kimiyya da fasahar kasa da kasa na birnin Beijing da aka shirya har sau goma ya riga ya zama wata kyakkyawar hanya da ake bi wajen yin ma'amala a tsakanin unguwar bunkasa tattalin arziki da fasaha ta Beijing da shahararrun masana'antu na gida da waje. Ta hanyar bikin baje kolin, Kamfanin Perstorp na hada magunguna na kasar Sweden da Kamfanin GE na Amurka da Kamfanin BOE na Beijing da Kamfanin China Netcom da sauran shahararrun kamfanonin gida da na waje sun kafa hedkwatocinsu ko cibiyoyin bincike a unguwar bunkasa tattalin arziki da fasaha ta birnin Beijing. Madam Yao Jing ta kara da cewa, "lalai, bikin baje koli na kimiyya da fasahar kasa da kasa na Beijing ya zama kyakkyawar hanya ce da muke bi cikin dogon lokaci wajen jawo kudaden jari, sa'an nan kuma muna sa kaimi ga kara zuba kudaden jari a unguwarmu ta hanyar farfaganda da muke yi a gun bikin baje koli da a kan shirya a ko wace shekara."
An ruwaito cewa, yanzu, masana'antun kera kayayyakin sadarwa da na motoci da na'urori da hada magungunan sha sun riga sun zama ginshikin masana'antun unguwar. Malam Zhang Boxu, shugaban hukumar kula da harkokin unguwar ya bayyana cewa, unguwar tana kan matsayi mai rinjaye a fannin kimiyya da fasaha da kwararru da labaru da sauransu, kuma tana samar da kyawawan guraben zuba jari. Kazalika hukumar tana yin hidima sosai ga masana'antu da aka kafa a unguwar. Ya kara da cewa,
"bisa manufarta game da mayar da moriyar masana'antu a gaban kome, hukumar kula da harkokin unguwar ta yi ta fito da sabbin hanyoyi da take bi wajen kyautata aikinta don yi wa masana'antu hidima. Makasudin hukumar shi ne domin masana'antu da aka kafa a unguwar za su kara samun bunkasuwa, su kara cin ribarsu mai tsoka."
Bisa shirin da aka yi, zuwa shekarar 2010, za a raya unguwar tattalin arziki da fasaha ta birnin Beijing don ta zama wani sabon gari wanda masana'antun zamani zai zama ginshikinta ta yadda za ta fuskanci kasuwannin kasa da kasa.(Halilu) 1 2
|