Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-03 15:33:17    
Ana cin gajiyar bikin baje koli na kimiyyar kasa da kasa don raya unguwar bunkasa tattalin arziki da fasaha ta Beijing, babban birnin kasar Sin

cri

A shekarar 1992, an kafa unguwar bunkasa tattalin arziki da fasaha ta Beijing wato BDA a wurin "Yizhuang" da ke a kudancin birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. A gun bikin baje koli na kimiyya da fasahar kasa da kasa na Beijing da aka shirya a karo na farko a shekarar 1998, an cim ma yarjejeniyoyi kan ayyuka 6 don kafa masana'antu a unguwar. Yanzu, masana'antun da aka kafa bisa yarjejeniyoyin da aka daddale a gun irin wannan bikin baje-koli sun riga sun zama ginshikin aikin masana'antu a unguwar.

A gun bikin baje-koli na kimiyya da fasahar kasa da kasa na karo na 10 na Beijing da aka rufe a kwanakin baya ba da dadewa ba, unguwar ta nuna wa jama'a manufofi da za ta bi wajen raya ta ta hanyar zamani. Madam Yao Jing, jami'ar hukumar kula da harkokin unguwar ta bayyana cewa, "a gun bikin baje-koli na kimiyya da fasahar kasa da kasa da aka shirya a bana, an gwada kyakkyawan sakamako da unguwarmu ta samu wajen neman bunkasa masana'antun kera kayayyakin sadarwa da motoci da na'urori da na hada magungunan sha da sauransu, muna fatan unguwarmu za ta kasance a sahon gaba a yankunan raya tattalin arziki da fasaha na matakin kasa."


1 2