A shekarar 1982 da ta gabata, an raya wurin yawon shakatawa na Zhangjiajie zuwa wurin shan iska na gandun daji na kasar Sin bisa shirin da aka tsara. Fadinsa ya kai misalin murabba'in kilomita dubu 13. Duk wannan wurin shan iska wuri ne mai tsarin kasa na limestone, kuma ba a taba yin amfani da shi ba tukuna. Ana iya ganin itace da namun daji ire-ire fiye da 500 a wajen. Itace masu daraja sun hada da gingko da dove tree da dawn redwood, sa'an nan kuma, namun dajin suna hada da civet cats da birai da tsuntsaye da salamanders da dai sauransu.
Dadin dadawa kuma, kananan kabilu 3 na kasar Sin wato kabilun Tujia da Bai da kuma Miao suna yin zaman tare cikin jituwa a wannan wurin shan iska na Zhangjiajie, wadanda yawansu ya kai misalin kashi 70 cikin kashi dari, bisa jimlar mazaunan wurin. Ko da yake kabilar Han da ta sami rinjaye a kasar Sin tana ba da babban tasiri ta fuskar al'adu a wajen sannu a hankali, amma wadannan kananan kabilu 3 suna cin gaba da bin yawancin al'adun gargajiyarsu, kamar su, harsuna da bukukuwa da tufafi da hanyoyin da suke bi a fannin aikin gona da dai makamantansu.
A shekarar 1992 da ta zarce, Hukumar ilmi da kimiyya da al'ada ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta tanadi wurin yawon shakatawa na Wulingyuan da ke lardin Hunan na kasar Sin a cikin takardar jerin sunayen wuraren tarihi na duniya.(Tasallah) 1 2
|