Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-30 15:47:24    
Britaniya ba za ta nisanci Amurka ba in ji Gordon Brown

cri

Da farko,a cikin jawaban da suka yi baya bayan nan,wasu manyan jami'an gwamnatin Britaniya sun sha bayyana cewa watakila za a samu sauyi cikin dangantakar dake tsakanin Britaniya da Amurka,kafofin yada labarai sun bayyana cewa wannan alama ce da Brown ya bayar na neman samu martani.wadannan jawaban da manyan jami'an Britaniya suka yi sun jawo damuwar Amurka wadda ta fi sa lura kan manufofin gwamnatin Brown,abin da ya fi dame Amurka shi ne majalisar dokoki ta Britaniya za ta ba da shirin janye sojojinta daga Iraq,shi ya sa hukumomin Amurka sun sha bukatar Brown ya bayyana matsayinsa a fili.Bisa wannan matsin lamba Brown ya fara ziyararsa a Amurka a karshen watan Yuli kafin lokacin da ya tsara a watan Satumba.Har ma ya fito fili ya bayyana cewa Gwamnatinsa ba za ta raunana dangantakar dake tsakaninta da Amurka ba akasin haka za ta karfafa wannan dangantaka dake tsakaninsu domin kawar da damuwar Amurka da kwantar da hankulan kafofin yada labarai kan tsammanin da suke yi kan wannan dangantaka.

Na biyu,cikin wata daya da 'yan kai bayan da ya haye kujerar mulki,Brown ya nuna karfin zuciyarsa wjen kawo sauyi a cikin harkokin gida har ma ya samu yabo mai yawa.Kwanan baya an samu babbar ambaliyar ruwa da ba a taba ganin irinta ba cikin shekaru sittin da suka shude,wannan ya ba shi damar samu yabo.Bisa sakamakon binciken ra'ayoyin jama'a da aka buga a cikin jaridar "daily telegram" ta ran 27 ga wata,an ce Brown ya samu goyon baya da kashi 41 bisa dari,ya fi David Cameron,shugaban Jam'iyyar conservative party yawa da maki tara bisa dari,wannan babbar nasara ce da jam'iyyar labour party ta samun tun bayan yakin Iraq.

Na uku,mummunan tasirin da gwamnatin labour party ta haddasa saboda yakin Iraq ya ragu sosai,mutanen Britaniya da ke da tarihin mulkin mallaka na daruruwan shekaru ba sa lura kan shirin gwamnatin na janye sojoji daga Iraq.Kafin ya hau kujerar mulki,Brown ya je Iraq shi kansa domin binciken lamuran dake tafiya a Iraq da nufin fadakar da jama'ar kasa zai canza manufar kan Iraq.Amma a halin yanzu wannan matsin lamba bai kawo razana ga mulkinsa da kwarjininsa na siyasa kai tsaye ba,daidaita manufar gwamnatinsa kan Irq ba shi da muhimmanci ga Brown.Ga shi a halinyanzu babu wani zabi illa ya ci gaba da bin manufar Blair kan kasar Iraq domin farantawa Amurka rai Manazarta sun yi nuni da cewa shi Brown yana da sha'awa sosai kan tarihi da siyasa na Amurka,ya kan yi mu'amalla sosai da shugabannin siyasa na Amurka,shi firayim ministan Britaniya mai kishin Amurka.Brown ya fi Blair kwarewa wajen tafiyar da harkokin mulki.yana da dabarun gamsar da Amurkawa,kuma yana da dabarun kare kwarjinin mutanen Ingila.Manazarta sun yanke shawara cewa gwamnatin Brown za ta jada dangantaka dake tsakanin Britaniya da Amurka baya ba.(Ali)


1 2