Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-30 15:47:24    
Britaniya ba za ta nisanci Amurka ba in ji Gordon Brown

cri

Firayim ministan Britaniya Gordon Brown ya tashi zuwa Amurka a ran 29 ga wata,daga nan ya fara ziyararsa ta farko a kasar Amurka tun lokacin da ya haye karagar mulki.Kafin tashinsa ya bayyana a fili cewa Britaniya ba za ta nisanci Amurka ba.Kakakinsa shi ma ya gaya wa kafofin yada labarai cewa Brown ba zai gabatar da shirin janye sojojin Britaniya daga Iraq a cikin wannan ziyararsa ba,Sojojin Britaniya za su cigaba da kasancewa a yankin Basra dake kudancin Iraq har zuwa ranar da sojojin Iraq suka samu karfin kare zaman lafiyar wannan yankin.Kafofin yada labarai na Britaniya wadanda suke jiran gwamnatin Brown ta daidaita manufarta kan Amurka sun yi mamaki da ganin wannan matakin da gwamnatin Brown ta dauka.

Sanin kowa ne lokacin da Blair ke mulki,da akwai kyakkyawar dangantaka ta kut da kut tsakanin Britaniya da Amurka cikin shekaru da dama.Amma wani muhimmin dalilin da ya sa Blair ya sauka daga kujerar mulki shi ne ya kara kusantar juna tsakaninsa da Amurka har ma ya shiga yakin Iraq da Amurka ta jagoranta ba tare da kulawa da sakamako ba.Galibin mutane suna masu ra'ayin cewa Brown zai iya koyon darasi daga Blair bayan ya hau kujarar mulki,zai nisanci shugaba George.W.Bush,haka kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta rage karfi,abin mafi maiyiwuwa ne Britaniya za ta daidaita manufarta kan Iraq da farko.Duk da haka ra'ayin da Brown ya bayar kafin tashinsa zuwa Amurka ya sha banban da abin da ake bukata.Bayan da suka nazarci al'amuran duniya na yanzu,manazarta suna masu ra'ayin cewa Brown ya dauki wannan mataki ne bisa wasu muhimman dalilai.


1 2