Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-25 15:43:46    
Wadanda suka samu nasara a gasarmu ta kacici-kacici dangane da "Garin panda, lardin Sichuan"

cri

1. Ko asalin sunan kwarin Jiuzhaigou yana da nasaba da kauyuka 9 na 'yan kabilar Tibet da ke cikin wannan kwari ko a'a?

Kwarin Jiuzhaigou yana yammacin lardin Sichuan, kuma an nada ma wannan kwari mai zurfin kilomita fiye da 40 sunan Jiuzhaigou ne sabo da kasancewar kauyuka guda 9 na 'yan kabilar Tibet a wurin.

2. Ko an tanadi kwarin Jiuzhaigou da wurin shakatawa na Huanglong a kan takardar jerin sunayen wuraren tarihi na halitta na duniya?

E, haka ne, a shekarar 1992, kungiyar UNESCO, wato kungiyar kula da ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD ta tanadi kwarin Jiuzhaigou a kan takardar sunayen wuraren tarihi na hallita na duniya tare kuma da wani wuri daban mai ni'ima da ke da nisan kilomita 130 daga kwarin, wato Huanglong.

3. Tsawon shekarun wurin tarihi na Sanxingdui ya kai nawa?

A hakika, tsawon tarihinta ya kai har shekaru 2000.

4. A cikin abubuwan tarihi da aka tono daga karkashin Sanxingdui, mene ya fi nuna kyakkyawar fasahar zamanin da, ko abubuwan da aka yi da lu'u lu'u ne ko kuma wadanda aka yi su da tagulla?

To, amsa ita ce kayayyakin tagulla.

5.ko babban dutsen Emeishan na daya daga cikin wurare masu tsarki na addinin Buddah?

kwarai, dutsen Emeishan yana daya daga cikin shahararrun duwastu na kasar Sin, kuma ya shahara ne musamman sabo da al'adun addinin Buddha da yake da shi. A karni na farko, addinin Buddah ya yadu daga Indiya har zuwa babban dutsen nan na Emeishan, an kuma gina gidan ibada na addinin Buddah a nan wurin, wanda ya kasance irinsa na farko a kasar Sin. Daga baya, dutsen Emeishan ya zamanto daya daga cikin wurare masu tsarki ga mabiyan addinin Buddah na kasar Sin.

6.Tsayin mutum-mutumin babban Buddah na Leshan ya kai nawa?

Mutum-mutumin babban Buddah na dutsen Leshan kasancewarsa mutum-mutumin Buddah mafi girma a duniya, tsayinsa ya kai fiye da mita 70.

7.ko an mayar da babban dutse na Qingchengshan a matsayin mafari na addinin Taoism?

Haka ne, dutsen Qingchengshan na daya daga cikin muhimman wuraren da aka sami asalin addinin Taoism, wato addinin gargajiya na kasar Sin.

8.yaushe ne aka gina madatsar ruwa ta Dujiangyan?

Madatsar ruwa ta Dujiangyan aikin ruwa ne da ya fi tsufa a duniya, kuma an gina shi ne a shekaru 2000 da suka wuce, don magance ambaliyar ruwa, kuma daga cikin tsoffin ayyukan ruwa na duniya, ita kadai ne ake ci gaba da amfani da ita har yanzu.

9. A ina ne garin Panda yake?

Ba shakka, a lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, sabo da a nan ne dabbobin panda suka fi zama.

10.panda nawa ne suke da zama a cikin kungurmin daji da ke gandun daji na Wolong na kasar Sin?

A gandun daji na Wolong, ban da panda da ake kiwo, akwai wasu fiye da 100 da ke zama a cikin kungurmin daji da ke cikin gandun dajin din.


1 2 3