Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-25 15:43:46    
Wadanda suka samu nasara a gasarmu ta kacici-kacici dangane da "Garin panda, lardin Sichuan"

cri

Idan ba ku manta ba, tun daga ranar 28 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, mun bude wata gasar kacici kacici dangane da lardin Sichuan na kasar Sin, wanda ya kasance gari ne na dabbobin panda, kuma a watan Afrilu na wannan shekara, an kawo karshen gasar tare da samun dimbin sakonnin masu sauraronmu. Dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin muna godiya ga wadannan masu sauraronmu da suka nuna himma da kokarin shiga gasar, mun gode. A hakika, bayan sakonnin amsoshin gasar, mun kuma sami sakonni da yawa da masu sauraronmu suka turo mana, inda suke alla-allan neman sakamakon gasar. To, yanzu muna farin cikin sanar muku da cewa, ga shi mun gama dudduba amsoshin da kuka turo mana, kuma sakamakon gasar ya fito. Sai dai da farko, bari mu dan maimaita muku gasar da muka yi.

Lardin Sichuan yana kudu maso yammacin kasar Sin, kuma kasancewarta gari ne na dabbobin panda. A cikin gasar, mun kai ku ziyara a wurare daban daban na lardin, don ku sami cikakkiyar fahimta a kan wurin daga dukan fannoni. Bayan bayanai a kan wadannan wurare daban daban, mun kuma gabatar muku da tambayoyi goma. To, yanzu bari mu maimaita muku tambayoyin daya bayan daya.


1 2 3