Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-24 16:25:51    
An bude taro kan batun sabuwar yarjejeniya ta kungiyar EU a tsakanin gwamnatoci

cri

Tun bayan da kasashen Faransa da Netherlands suka ki amincewa da "yarjejeniyar tsarin mulkin kungiyar EU" daya bayan daya ta hanyar kada kuri'ar raba gardama a shekarar 2005, kungiyar ta tsunduma cikin mawuyacin hali wajen kafa tsarin mulkinta a cikin shekaru biyu da suka wuce. Bayan da kasar Jamus ta zama kasa mai shugabancin kungiyar EU a farkon shekarar nan, ta mayar da sake fara aikin tsara tsarin mulkin a gaban kome. Bayan da aka dade ana tattaunawa cikin mawuyacin hali, daga bisani shugabannin kasashe daban daban sun sami sulhuntawa a gun taron koli da aka shirya a watan jiya, sun amince da shirin taswirar musamman domin kulla sabuwar yarjejeniya a maimakon yarjejeniyar tsarin mulkin kungiyar EU, ta haka an dakatar da ricikin tsara tsarin mulkin kungiyar.

Amma a ranar da aka fara yin taron tsakanin gwamnatoci, Anna Fotyga, ministar harkokin waje ta kasar Poland wadda ta halarci taron ministocin harkokin waje na kungiyar EU ta bayyana wa manema labaru cewa, a gun taron tsakanin gwamnatoci, kasarta za ta nemi da a yi bayani a kan batun tsarin kada kuri'a na majalisar kungiyar Eu da aka tanada cikin daftarin sabuwar yarjejeniyar. Ko da yake wannan ya damu kungiyar EU a wasu fannoni. Amma Hans-Gert Poettering, shugaban majalisar Turai ya yi gargadi ga kasashen kungiyar cewa, "zartas da sabuwar yarjejeniyar babban tabbaci ne da za a bayar don kara yadada dimokuradiyya a cikin kungiyar EU, da kuma kyautata ayyukanta, sabo da haka kamata ya yi, dukkan kasashen kungiyar su nuna girmamawa ga alkawarinsu da kuma cika shi.(Halilu)


1 2