Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-24 16:25:51    
An bude taro kan batun sabuwar yarjejeniya ta kungiyar EU a tsakanin gwamnatoci

cri

Ran 23 ga wata, a babban zauren kungiyar tarayyar Turai wato EU da ke a birnin Brussels, hedkwatar kasar Belgium, an bude taron kungiyar EU a tsakanin gwamnatoci musamman domin tattaunawa kan kundin sabuwar yarjejeniya da zai mamaye gurbin "yarjejeniyar tsarin mulki na kungiyar EU. Wannan ya alamanta cewa, an sake fara yin aikin kafa tsarin mulkin kungiyar wanda aka dakatar da shi a cikin shekaru biyu da suka wuce.

Taron ministocin harkokin waje na kungiyar EU wanda aka yi a wannan rana ya sanar da bude taron a tsakanin gwamnatoci, sa'an nan kasar Portugal wadda yanzu ke shugabancin kungiyar EU, kuma ke kula da harkokin rubuta sabuwar yarjejeniyar ta gabatar wa taron daftari na farko na sabuwar yarjejeniyar. Bisa iznin da majalisar kungiyar EU ta bayar, kungiyar aiki da ke kunshe da masanan dokoki na kasashe 27 na kungiyar EU za su yi taro na farko a ran 24 ga wata, don fara gudanar da hakikanan harkokin taro a tsakanin gwamnatoci. Babban aikin taron a tsakanin gwamnatoci shi ne, kyautata da yanke shawara kan kundin sabuwar yarjejeniyar a fannin dokoki da fasaha, bai kamata a sake tattaunawa kan manyan ka'idoji da hakikanan abubuwa na sabuwar yarjejeniyar wadanda kasashe daban daban suka riga suka amince da su a gun taron koli na kungiyar EU da aka yi a watan jiya ba. A ran 18 ga watan Oktoba mai zuwa, kasar Portugal za ta shugabanci wani taron koli na kungiyar EU a birnin Lisbon, don yanke shawara kan kundin karshe na sabuwar yarjejeniyar, ta yadda kasashe daban daban za su amince da shi da kuma fara aiki da shi kafin zaben majalisar Turai da za a yi a watan Yuni na shekarar 2009.

A gun bikin bude taron a tsakanin gwamnatoci, Luis Amado, ministan harkokin waje na kasar Portugal ya jaddada cewa, a muhimmin lokacin da ake fuskantar kalubale mai tsanani iri daban daban, kungiyar EU tana dokin yin kwaskwarima kan tsarinta. Ya ce, bisa matsayinta na kasar da ke shugabancin kungiyar a yanzu, kasar Portugal za ta aiwatar da iznin da ta samu daga majalisar kungiyar EU don ba da tabbaci ga yin taron tsakanin gwamnatoci yadda ya kamata, haka kuma za ta yi amfani da duk damar da za ta iya samu wajen neman samun nasarar kulla sabuwar yarjejeniya a fannin siyasa.


1 2