Bayan da suka yi nazari kan sanadai iri daban daban tare, masu bincike sun samar da hukunci cewa, idan iyaye mata ba su ciyar da yaransu da nononsu cikin dogon lokaci ba, to, yaransu za su kara fuskantar matsalar nauyi, amma idan sun yi watanni fiye da 3 suna ciyar da yaransu da nononsu, to, za a rage wa yara rabin barazanar fama da kiba.
Masu bincike sun bayar da wannan sakamakon bincike a cikin wata mujallar kasar Amurka, mai suna 'yin jiyya ga masu sukari', wadda aka fito da ita a kwanan baya. Kafin wannan kuma, wadannan masu bincike daga kasar Jamus sun taba gano cewa, yara sun kara fuskantar yiwuwar fama da kiba, saboda iyayensu mata sun fama da kiba, sa'an nan kuma, jariran da aka haife su ba da dadewa ba sun yi fiye da nauyi saboda sun fi yin girma a lokacin da suke cikin cikin iyayensu mata.(Tasallah) 1 2
|