Masu ciki da suka kamu da ciwon sukari a lokacin da suke da ciki su kan haifi jarirai masu nauyin jiki, ta yadda za a sa yara su kan fama da kiba. Amma sakamakon bincike mai dumi dumi da aka yi ya shaida cewa, idan iyaye mata sun ciyar da jariransu da nononsu, to, za a rage wa yara da yiwuwar fama da kiba.
Masu bincike na kasar Jamus sun yi bincike kan jariran da mata 324 suka haife su, wadanda suka kamu da ciwon sukari a lokacin da suke da ciki. A karshe dai sun gano cewa, a lokacin jarirtaka, jariran da ba a ciyar da su da nonon iyayensu mata ba da yawansu ya kai kashi 37 cikin dari nauyinsu ya wuce kima; wadanda aka ciyar da su da nonon iyayensu mata da yawansu ya kashi 28 cikin dari nauyinsu ya wuce kima, a cikinsu kuma, yawan wadanda iyayensu mata ba su ciyar da su da nononsu har tsawon watanni 3 ba, kuma nauyinsu ya wuce kima ya kai kashi 32 cikin dari, amma jariran da iyayensu mata suka yi watanni fiye da 3 suna ciyar da su da nononsu da yawansu ya kai kashi 22 cikin dari nauyinsu ya wuce kima.
1 2
|