Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-24 15:39:35    
Hasumiyar Huanghelou a lardin Hubei

cri

A cikin karni da dama da suka wuce, wannan hasumiya ta sha rugujewa a sakamakon yake-yake da gobara. Babbar gobara ta ragargaza ta duka a shekarar 1884. A cikin daular zamanin Qing na kasar Sin wato yau da shekarar 1644 zuwa ta 1912 kawai, an sake gina ta ko kuma yin mata kwaskwarima sau 4. Amma saboda tabarbarewar wata hukuma a lokutan baya ba ta iya sake gina wannan hasumiya yadda ya kamata ba. Masu yawon shakatawa sun iya ganin kyan ganin hasumiyar Huanghelou a cikin zane-zane da rubutattun wakoki kawai.

Bayan da kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen duniya a shekarar 1978, hukumar Wuhan ta sake gina wannan hasumiya bisa tsoffin fayil-fayil da hotuna a shekarar 1986. A kusa da sabuwar hasumiyar Huanghelou, akwai wata farar hasumiyar addinin Buddha, wadda aka gina a zamanin daular Yuan, wato a tsakanin shekarar 1279 zuwa ta 1368.(Tasallah)


1 2