Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-24 15:39:35    
Hasumiyar Huanghelou a lardin Hubei

cri

Hasumiyar Huanghelou da ke birnin Wuhan na lardin Hubei na daya daga cikin muhimman hasumiyoyi 3 na kasar Sin daga gabashin kogin Yangtze, saura 2 su ne hasumiyar Yueyanglou a birnnin Yueyang lardin Hunan da kuma hasumiyar Tengwangge a birnin Nanchang na lardin Jiangxi. A ko wace shekara dubban masu yawon shakatawa na gida da na waje suna kai mata ziyara.

Wannan hasumiya ta shahara a fannin aikin soja har tsawon shekaru fiye da 1700 saboda in an tsaya a hasumiyar, ana iya hangen kogin Yangtze duka.

Ma'anar Huanghe a Sinance ita ce rawayar gauraka, Lou kuma shi ne hasumiya. Akwai wata kyakkyawar almara game da asalin hasumiyar Huanghelou. An ce, a can da kyan karkarar wajen ya taba burge wata mala'ikar da ke hawan wata rawayar gauraka, shi ya sa ake kiran wannan hasumiya hasumiyar Huanghelou, wato hasumiyar da ke jawo hankalin wata mala'ikar da ke hawan wata rawayar gauraka.


1 2