Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-23 14:53:35    
Matsalolin da aka yi ta yi garkuwa da mutane a Afghanistan tana jawo hankulan duniya

cri

Sannan, kungiyar Taliban ta sake farfadowa a kasar Afghanistan, wannan al'amari ya bayyana cewa, matakin soja ba hanya ce kawai ba wajen daidaita batun tsaron kasar Afghanistan. Hakikanan abubuwa sun shaida cewa, ya kasance da ra'ayoyi daban-daban a cikin kawancen yin yaki da ta'addanci da ke karkashin jagorancin kasar Amurka kan yadda za a yi yaki da kungiyar Taliban ta hanyar soja. Wasu muhimman kasashen NATO ba su son tura sojojinsu zuwa yankunan kudu da gabashin kasar Afghanistan domin yin yaki da masu dauke da makamai wadanda suke adawa da gwamnatin Afghanistan kai tsaye. Sabo da haka, rundunar sojan kungiyar NATO da ke kasar Afghanistan wadda ba ta da isassun dakaru ta kara shiga mawuyacin hali.

Daga karshe dai, domin halin rashin kwanciyar hankali da ake ciki a kasar Afghanistan yana tsananta, kuma kasashen duniya ba su iya cika alkawuran samar wa kasar taimako domin sake raya ta ba, har ma gwamnatin kasar ba ta iya daidaita batutuwa iri iri cikin sauri kamar yadda ya kamata ba, yanzu ayyukan sake raya kasar Afghanistan suna samun cigaba sannu a hankali. Sakamakon haka, zaman rayuwar jama'ar Afghanistan ba ta iya samun kyautatuwa ba, wannan yana kawo illa ga goyon bayan da jama'a suke nuna wa gwamnatin. A waje daya, sabo da tattalin arziki da zaman al'ummar kasar ba su samu kyautatuwa ba, wanann ya haddasa bunkasuwar tattalin arziki irin na miyagun kwayoyi a kasar. Kungiyoyi masu adawa da gwamnati, ciki har da kungiyar Taliban suna samun arziki daga irin wannan tattalin arziki irin na miyagun kwayoyi. Sabo da haka, ana kara nuna damuwa ga irin wannan halin rashin kwanciyar hankali da na siyasa da ake ciki a kasar Afghanistan a nan gaba. (Sanusi Chen)


1 2