Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-23 14:53:35    
Matsalolin da aka yi ta yi garkuwa da mutane a Afghanistan tana jawo hankulan duniya

cri

A ran 22 ga wata da maraice, Yousuf Ahmadi, kakakin kungiyar Taliban wadda ke adawa da gwamnatin kasar Afghanistan ya bayyana cewa, domin gwamnatin kasar Koriya ta kudu tana kokarin yin mu'amala da ita, kungiyar Taliban ta tsai da kudurin kara sauran sa'o'i 24 ga mutane 23 na kasar Koriya ta kudu da aka yi garkuwa da su da ta taba tsai da kudurin kashe su a ran 22 ga wata da dare. Wannan sabon cigaba ne da aka samu game da matsalar yin garkuwa da mutanen kasar Koriya ta kudu da kungiyar Taliban ta yi. Amma matsalolin da suka sa a kan yi garkuwa da mutanen kasashen waje da su kan auku a kasar Afghanistan suna jawo hankulan kasashen duniya sosai.

Domin yanzu halin rashin kwanciyar hankali da ake ciki a kasar Afghanistan yana tsananta sosai, an riga an haddasa wasu matsalolin yin garkuwa da mutanen kasashen waje da 'yan kasar a Afghanistan a cikin shekarar da muke ciki. Manazarta suna ganin cewa, domin kungiyar Taliban ba ta da karfin yin gwagwarmaya da dakarun gwamnati da sojojin kasashen waje da ke kasar ta hanyar soja, kungiyar Taliban tana yunkurin bata karfin yin yaki da ta'addanci da ayyukan sake raya kasar da ake yi ta hanyoyi iri daban-daban, ciki har da hanyar yin garkuwa da mutane. Ana ganin cewa, za a ci gaba da yin irin wannan gwagwarmaya a tsakanin kungiyar Taliban da gwamnatin Afghanistan. Halin da ake ciki a kasar a fannin kwanciyar hankali ba zai samu kyautatuwa a cikin wasu lokuta masu zuwa ba.

Da farko dai, gwamnatin Afghanistan da ke karkashin jagorancin Hamid Karzai tana fuskantar matsin lamba daga kasashen waje da kungiyoyin kasar domin matsalolin yin garkuwa da mutane da su kan faru a kasar. Lokacin da ake ceton mutanen kasashen waje da aka yi garkuwa da su, da farko dai gwamnatin Karzai tana fuskantar matsin lamba daga gwamnatocin kasashen waje da suka girke sojojinsu a kasar. Bayan da aka saki mutanen kasashen waje, tana kuma fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin siyasa na kasar. Mutane sun kai wa gwamnatin suka, cewar bai kamata gwamnatin ta nemi sulhuntawa da 'yan ta'adda ba. A waje daya, ya kamata gwamnatin ta mai da hankali kan 'yan kasar wadanda aka yi garkuwa da su kamar yadda take mai da hankali kan mutanen kasashen waje da aka yi garkuwa da su. Bugu da kari kuma, a cikin majalisar dokokin kasar Afghanistan, ana ta kiran gwamnatin da ta yi shawarwari da kungiyar Taliban. Sabo da haka, gwamnatin Karzai ta shiga mawuyacin hali lokacin da take tsara manufofin tabbatar da kwanciyar hankali a kasar.


1 2