Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-18 16:59:40    
Kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta duniya

cri

Da ma, a farkon kafuwarta, kasashe biyar ne kawai ke cikin kungiyar, wadanda suka hada da Birtaniya da Faransa da Italiya da Japan da kuma Amurka. Daga baya, kungiyoyin sun yi ta karuwa har zuwa 185 a yanzu, wato ke nan kusan kowace kasa a duniya na da nata kungiyar agaji ta Red Cross ko Red Crescent.

Kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta kafu a shekarar 1904, kuma bayan kafuwarta, har kullum, tana gudanar da harkokinta a fannin jin kai, ta kuma sami goyon baya daga gwamnatin kasar da kuma al'ummar kasar. Yanzu kungiyar tana da rassanta 31 a matsayin lardi da kuma guda biyu a yankunan musamman na Hongkong da Macao.

Kamar yadda muka sani, red cross da red crescent alamu biyu ne da kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ke yin amfani da su wajen gudanar da harkokinta, amma a ran 14 ga watan Janairu na shekarar 2007 da muke ciki, kungiyar ta kuma fara aiki da wata sabuwar alama da aka fi sani da "Red Crystal", wadda kuma ta tashi daya da alamun "Red Cross" da "Red Crescent". Alamar Red Crystal ta samar da sauki ga Isra'ila wajen gudanar da harkokin agaji, sabo da tun daga shekarar 1949, kungiyar agaji ta Red Shield of David ta Isra'ila tana neman shiga kungiyar Red Cross da Red Crescent ta duniya, amma sabo da dalilin addini, ta ki yarda da yin amfani da alamun Red Cross da Red Crescent.(Lubabatu)


1 2 3