Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-18 16:59:40    
Kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta duniya

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama Amina Abubakar, wadda ta fito daga birnin Maiduguri da ke jihar Borno, tarayyar Nijeriya. Malama Amina Abubakar ta turo mana wata wasika a kwanan baya, inda ta ce, ina so a binciko mini tarihin kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent, shin yaushe ne aka kafa ta? Domin amsa tambayar, a cikin shirinmu na yau, bari mu ba ku takaitaccen bayani dangane da kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent.

Hadaddiyar kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta duniya kungiyar jin kai ce mai zaman kanta, wadda kuma ba ta gwamnati ba. Ita hadaddiyar kungiya ce ta kungiyoyin Red Cross da na Red Crescent na kasashe daban daban, kuma hedkwatarta tana birnin Geneva.

An fito da ra'ayin kafa kungiyar agaji ta Red Cross a shekarar 1859. A lokacin, Henry Dunant, dan kasar Switzerland ya gane ma idonsa kazamin fada da aka yi tsakanin sojojin daular Austria da kawancen Franco-Sardinian a Solferino, Italiya, inda mutane dubu hudu suka mutu ko kuma ke bakin mutuwa, a yayin da wadanda suka jikkata ba su iya samun magani ba. A lokacin, Mr.Dunant ya jagoranci mutanen wurin da su yi wa sojojin jiyya da ciyar da su da kuma sanyaya musu rai. Bayan dawowarsa kuma, Mr.Dunant ya yi kira da a kafa kungiyar agaji don ba da taimako ga wadanda suka jikkata a fagen yaki. Sabo da haka, a shekarar 1863, kwamitin Red Cross ya kafu. Sa'an nan, kasashen duniya, musamman ma kasahsen Turai da Amurka sun kafa kungiyoyin Red Cross bi da bi.


1 2 3